Zargin Badaƙalar N2.7bn: Kotu Ta Karɓi Ƙarin Shaidu a kan Tsohon Ministan Buhari
- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da karɓar wasu takardu a matsayin hujjoji a shari’ar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika
- Wannan na nuni da cewa hukumar EFCC na ƙara matsa lamba wajen samo bayanai da za su iya ƙarfafa tuhumar da take yi masa kan zargin almundahana
- EFCC na zargin Hadi Sirika, da 'yarsa Fatima Sirika, da surukinsa, Sule Hamma da wani kamfani da karkatar da zunzurutun kudi har Naira biliyan 2.7
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mai shari’a S.C. Oriji na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya amince da ƙarin shaidu da ake gabatarwa a shari’ar da ake yi da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ke gurfanar da Sirika tare da ’yarsa Fatima Sirika, surukinsa Jalal Sule Hamma da kamfanin Al Buraq Global Investment Limited.

Asali: Twitter
A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, EFCC ta bayyana cewa tana gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume guda shida da suka shafi almundahanar kudi N2.7bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Kotu ta karɓi hujjoji a kan Ministan Buhari
A cewar sanarwar kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, yayin zaman kotun na ranar Litinin, lauyan masu gabatar da ƙara, A.O. Atolagbe, ya gabatar da shaida na tara.
Wannan shaida dai tsohon babban manaja ne a ɓangaren Gudanarwa da Kula da Ma’aikata na Hukumar Kula da Nukiliya ta Najeriya (NNRA), wanda ya tabbatar da karbar wasikar EFCC a kan binciken.
Ya bayyana cewa ya rubuta wa hukumar wasiƙa yana bayyana cewa Hamma ma’aikacin NNRA ne da aka ɗauka a watan Nuwamban 2021, amma ya ajiye aiki bayan shekara biyu.
Bayanan da ya tura wa EFCC sun haɗa da wasiƙar ɗaukar Hamma aiki, wasiƙar neman barin aiki, amincewar hukumar NNRA da sauran bayanan da aka nema.

Asali: Facebook
Shaidan ya ce dukkan waɗannan takardu an rubuta su ne a kan takardar ofishin NNRA kuma ya sa hannu a kansu.
Tsagin Minista ya soki bukatar EFCC
Lauyan EFCC, Atolagbe, ya nemi kotu ta amince da waɗannan takardu a matsayin shaida, amma lauya mai kare Hamma, Sanusi Musa, SAN, da wanda ake ƙara na huɗu, M.J. Numa, SAN, sun yi ƙalubalanci hakan.
Musa ya dogara da Sashe na 104 na Dokar Shaidu, yana mai cewa takardun ba su da muhimmanci a shari’ar.
Ya kuma ce banda shafi na ɗaya da na biyu, sauran ba a tabbatar da su a matsayin sahihan kwafin asali ba, kuma ba a biya kuɗin tabbatar da sahihancinsu ba.
Kotu ta dage sauraron shari’ar Ministan Buhari
Bayan sauraron korafe-korafen lauyoyi, Mai shari’a Oriji ya amince da karɓar takardun a matsayin shaida bayan an tabbatar da sahihancinsu.
Alkalin ya kuma bayar da umarnin a biya kuɗin da ake buƙata don samun sahihan kwafin takardun. Kotu ta dage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 6 ga Mayu, 2025.
EFCC na ci gaba da binciken tsohon Minista
A baya, mun ruwaito cewa Hukumar EFCC ta bayyana wa kotu cewa Fatima Sirika, diyar tsohon ministan sufurin jiragen sama, na da hannu a cikin zargin badakalar kwangila.
Ana zargin tsohon Ministan a gwamnatin Muhammadu Buhari da hada kai da wasu wajen tafka badakalar kwangila da yawan kudin ya kai akalla Naira biliyan 1.14 a zamaninsa.
Bayanin ya fito ne yayin zaman kotu da ya gudana a gaban Mai shari’a Sylvanus Oriji, inda EFCC ta gabatar da shaidarta ta biyu, jami’in kula da harkokin bankin Zenith, Mishelia Arhyel.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng