Gwamnatin Kano Za Ta Sayowa Sanusi II Motoci da Kudin Kananan Hukumomi

Gwamnatin Kano Za Ta Sayowa Sanusi II Motoci da Kudin Kananan Hukumomi

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta shirya ƙayata masarautar Kano a ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Sanusi II
  • An umarci ƙananan hukumomi da su fitar da kuɗaɗe domin gyarawa da sayo sababbin motoci ga masarautar Kano
  • Kowace daga cikin ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar za ta ba da na ta kason domin gudanar da aikin wanda zai laƙume N670m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta shirya gyarawa tare da sayan sababbin motoci ga masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Gwamnatin ta umarci kowace daga cikin ƙananan hukumomi 44 da ke fadin jihar da su bayar da gudummawar kimanin Naira miliyan 15.2, jimillar Naira miliyan 670, domin sayowa da gyara motocin.

Sanusi II
Gwamnatin Kano za ta gwangwaje Sanusi II da motoci Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa wacce daraktan bincike na ƙananan hukumomi, Abubakar S. Dabo ya fitar a madadin kwamishina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Gwamnati za ta sayowa Sanusi II motoci

"An umurce ni da na sanar da amincewar gwamnati kan fitar da jimillar ƙudi na N15,227,272.72 daga kowace ƙaramar hukuma, domin gyaran motoci guda biyu da kuma samar da sababbin motoci guda huɗu ga masarautar Kano ta hannun kamfanin Sottom Synergy Resources Ltd.”

- Abubakar S. Dabo

Bayani kan yadda za a kashe kuɗin ya nuna cewa Naira miliyan 670 ɗin za a yi amfani da su ne wajen gyaran tsohuwar motar Rolls Royce ta shekarar 1969 (DH 420), farfaɗo da motar Cadillac limousine, da kuma sayen sababbin motoci huɗu ƙirar Toyota Land Cruiser VXR (2024 full option).

Wasiƙar ta kuma umarci shugabannin ƙananan hukumomi da su tabbatar da bin ƙa’ida da doka wurin aiwatar da wannan umarni.

An samu saɓanin ra'ayi

Sai dai wannan matakin ya haifar da bayyana ra’ayoyi masu cin karo da juna.

Wasu daga cikin masu sukar wannan matakin, sun tambayi dalilin fifita kashe kuɗi kan kayan alatu na sarauta a lokacin da mafi yawan ƙananan hukumomi ke fama da matsin tattalin arziki da rashin manyan ababen more rayuwa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano za ta gyarawa Sanusi II motoci Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A gefe guda kuma, masu goyon bayan wannan mataki sun bayyana cewa hakan alama ce ta ƙudirin gwamnatin jihar wajen dawo da martaba da ingancin aikace-aikacen masarautar Kano, musamman bayan dawo da Sanusi II a matsayin Sarki.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan ƙorafin da jama'a ke yi ba.

Watakila za a rabawa sarakunan Kano, Rano, Gaya da Karaye motocin da za a sayo ne.

Gwamna Abba ya yi wa Baffa Bichi martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi martani kan kalaman da Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya yi na zargin ba Rabiu Kwankwaso kuɗaɗe.

Gwamna Abba ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta taɓa bayar da ko sisin kobo ba ga tsohon gwamnan na jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa tsohon sakataren na gwamnatin jihar Kano yana ƙoƙarin kawo rarrabuwar kai ne kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »