"Ba Zan Koma Majalisar Dattawa ba," Sanata Buhari Zai Nemi Kujerar Gwamna a 2027

"Ba Zan Koma Majalisar Dattawa ba," Sanata Buhari Zai Nemi Kujerar Gwamna a 2027

  • Sanata Abdulfatai Buhari ya bayyana burinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo a 2027, inda ya ce ya gaji da aikin majalisa
  • Dan majalisar ya ce ko da an kawo masa tikitin sanata, ba zai yi takara ba sai dai gwamna, sannan zai horar da wadanda za su gaje shi
  • Wani hadiminsa ya tabbatar da cewa mutanen Oyo suna son ya tsaya takarar gwamna a 2027, bayan ya yi wa'adi uku a matsayin sanata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Sanata Abdulfatai Buhari, mai wakiltar Oyo ta Arewa, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2027.

A wata hira da ya yi da Parrot FM, gidan rediyon da ke Oyo, jigon jam'iyyar APC ya ce a shirye yake ya hakura da aikin majalisa domin shugabantar jihar.

Sanata Abdulfatai ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo
Sanata Abdulfatai Buhari, dan majalisar dattawa mai son tsayawa takarar gwamnan Oyo. Hoto: @BuhariOyoNorth
Asali: Twitter

Sanata Buhari zai tsaya takarar gwamnan Oyo

Jaridar The Cable da ta bibiyi hirar, ta rahoto Sanata Buhari yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

"Wannan shi ne karo na uku da zan zama sanata kuma karo na hudu da zan je majalisar dokoki ta kasa. Ni kwararren dan majalisa ne kuma na gamsu da kwarewa ta.
"Amma burin da nake son cikawa na gaba, idan Allah ya ba ni dama, shi ne in zama gwamnan jihar Oyo."

Sanata Abdulfatai Buhari ya yi watsi da batun komawarsa majalisar dattawa, yana mai cewa ya gaji haka nan, ko da kuwa an kai tikitin sanatan zuwa karamar hukumarsa.

"Ko da sun sake kawo sanata yankinmu ko kuma aka ba Oke Ogun wani mukamin, ba zan sake fitowa takarar sanata ba, sai dai gwamna.
"Mun bar wa 'yan baya su yi. Za mu horar da wasu daga cikin wadanda ke son yin wakilci a bayanmu. Za mu horar da duk wanda ya samu tikiti, kuma zai yi nasara."

- Sanata Abdulfatai Buhari.

"Mutanen Oyo ke so ya tsaya takara" - Kilani

Kafin wannan babbar sanarwa, jita-jita da hasashe sun yadu kan matakin siyasa na gaba da Sanata Buhari, daya daga cikin fitattun 'yan siyasar Kudu zai dauka.

Afeez Kilani, babban mataimaki ga sanatan, ya tabbatar da cewa ubangidansa zai tsaya takarar kujerar gwamnan Oyo a zaben shekarar 2027.

"Mutanen jihar Oyo suna son ya tsaya takarar gwamna a 2027. Bayan ya yi aiki na tsawon wa'adi uku a matsayin sanata, suna jin ya cancanci ya zama gwamna."

Harkar siyasar Buhari ta fara ne a 2003 lokacin da aka zabe shi a majalisar wakilai don wakiltar mazabun Ogbomoso ta Arewa/Ogbomoso ta Kudu/Oriire.

Dan majalisar dattawa daga Oyo ya yanke shawarar tsayawa takarar gwamnan jihar
Sanata Abdulfatai Buhari daga jihar Oyo. Hoto: @BuhariOyoNorth
Asali: Twitter

Takaitaccen tarihin siyasar Sanata Buhari

A shekarar 2015, yayin da yake aiki a matsayin kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta a karkashin marigayi Sanata Abiola Ajimobi, Sanata Buhari ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar sanata.

Ya samu nasara a wannan kuduri nasa, musamman saboda ‘guguwar’ siyasar Muhammadu Buhari da ta tashi a lokacin da ya lashe zaben shugaban kasa.

Bayan shekaru hudu da wannan nasara, ya nemi sake tsayawa takara a 2019 kuma ya doke Hon. Mulikat Adeola Akande, ‘yar takarar PDP wacce ita ma ta fito daga Ogbomoso.

Sannan 2023 ta zo, na ma ya samu nasara, inda ya zama mutum na farko da ya lashe zaben sanata na gundumar sau biyu a jere.

Kotu ta kwace kadarorin Sanata Buhari

A wani labarin, mun ruwaito cewa, AMCON ta karbe kadarorin Sanata Abdulfatai Buhari, kan bashin N600m da kamfaninsa ya karba daga GTBank.

Kotun Tarayya ta ba da umarnin kwace kadarorin sanatan biyo bayan rashin biyan bashin da ya karba, ta hanyar kamfaninsa, Abadat Ventures Limited.

Wasu dukiyoyin da AMCON ya kwace sun hada da: kadarori a 12, St, Petersburg Street, Wuse II, Abuja da Plot 516 off Misau Crescent, off Birnin Kebbi Crescent, Garki II, Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »