Jonathan Ya Sake Yin Magana kan Marigayi 'Yar'adua bayan Shekara 15 da Rasuwarsa

Jonathan Ya Sake Yin Magana kan Marigayi 'Yar'adua bayan Shekara 15 da Rasuwarsa

  • Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya faɗi kyawawan halayen mai gidan shi, tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Ƴar'adua
  • Jonathan, wanda ya yi aiki da Ƴar'adua ya bayyana marigayin a matsayin shugaba na gari, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al'umma
  • Ya ce duk da shekara 15 kenan da rasuwarsa, har yanzu ana koyi da kyawawan halayensa na hadin kai, zaman lafiya da, gaskiya da rikon amana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya tuna da marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, wanda ya rasu shekaru 15 da suka gabata.

Goodluck Jonathan ya bayyana shi a matsayin shugaba na gari kuma mai kishin kasa da jajircewa wajen hada kan al'umma.

Jonathan da Yar'adua.
Jonathan ya tuna da Umaru Musa Yar'Adu'a, ya fadi wasu daga cikin alherinaa ga Najeriya Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Tsohon shugaban, wanda ya riƙe kujerar mataimakin shugaban Najeriya a zamanin mulkin Yar'adua ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Marigayi Umaru Musa Yar'adu ya rasu ne a rana irin ta yau, 5 ga watan Mayu, 2010, wanda a yau ya cika shekara 15 da rasuwa.

Jonathan ya tuna da Umaru Musa Ƴar'adua

A cikin sanarwar, Jonathan ya bayyana Umaru Yar’Adua a matsayin shugaba wanda rayuwarsa ta kasance cike da hidima, sadaukarwa da kuma adalci ga al'umma.

Ya ce marigayin ya kasance shugaba mai gaskiya da rikon amana wanda ayyukansa suka dogara da kaunar kasa da biyayya ga doka.

A cewar Jonathan, duk da Yar'adua bai jima ba a kan mulki, amma ya ba da gudummuwar da ba za a manta da ita ba a tarihin Najeriya.

Abin da Jonathan ya ce kan Yar'adua

Dr. Goodluck Jonathan ya ce:

“A lokacin da yake matsayin shugaban kasa, Yar’Adua ya ɗauki nauyin hada kan al’umma, da gina kasa bisa tubalin gaskiya, zaman lafiya da ci gaba.
"Koda yake bai wani daɗe ba a kan mulki, zamaninsa ya kasance mai cike da tasiri da kuma kyakkyawan fata ga Najeriya.”

Jonathan ya kara da cewa, duk da shekara 15 kenan da rasuwarsa, har yanzu Yar’Adua ya ci gaba da zama abin koyi a shugabanci na gari.

Dr. Goodluck Jonathan.
Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya ƙara jimamin rasuwar Umaru Musa Ƴar'adua Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

'Halayen Ƴar'adua abin koyi ne' - Jonathan

Bugu da ƙari, tsohon shugaban ƙasar ya ce Marigayi Umaru Musa ya zama abin koyi wajen riƙon amana, zaman lafiya da gaskiya a harkokin gwamnati.

“Yau ina tunawa da abokina, dan uwana kuma shugabana, saboda rayuwarsa cike take da hidima da sadaukarwa.
"Kokarinsa wajen gina kasa, da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da dimokuradiyya mai adalci, da daidaito da hadin kai sun kasance abin koyi gare mi,” in ji Jonathan.

An karrama Jonathan da lambar yabo

A wani labarin, kun ji cewa Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya lashe kyautar Sunhak Peace ta 2025 saboda rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hadimin Jonathan na musamman, Ikechukwu Eze, ya fitar a Abuja a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce za a karrama tsohon shugaban Najeriya, Jonathan da kyautar ne a birnin Seoul, kasar Koriya ta Kudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »