Ruɗani: Muhammadu Sanusi II Ya Naɗa Sabon Galadiman Kano da Wasu Sarakuna 4

Ruɗani: Muhammadu Sanusi II Ya Naɗa Sabon Galadiman Kano da Wasu Sarakuna 4

  • Duk da jibge jami'an tsaro, sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya naɗa wa sabon Galadiman Kano da wasu mutum huɗu rawanin sarauta
  • Taron naɗin wanda ya gudana a fadar mai martaba sarki yau Juma'a, ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf, sarakuna da shugabannin addini
  • A ɗaya ɓangaren kuma an ruwaito cewa sarki na 15, Aminu Ado Bayero ya yi taron naɗin sabon Galadima a fadar Nassarawa duk a jihar Kano a yau

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya nada Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano.

Sarki Sanusi II ya naɗa wa sabon Galadima rawani tare da wasu sarakai huɗu yau Juma'a, 2 ga watan Mayu, 2025.

Muhammadu Sanusi II.
Sarki Sanusi II ya naɗa sabon Galadiman Kano Hoto: @MasarautarKano
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan naɗi na zuwa ne bayan rasuwar tsohon Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda ya koma ga Allah yana da shekaru 92.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Naɗin dai ya zo da rikici yayin da ɓangarori biyu da ke rigima, Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sarkin Kano na 15 suka naɗa Galadima biyu.

Sanusi II ya naɗa sabon Galadiman Kano

A ɓangarensa, Sarki Muhammadu Sanusi ya ayyana Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadima kuma a yau Juma'a aka yi taron naɗa masa rawani.

Sauran wadanda Sanusi II ya naɗa sun haɗa da Hakimin Nassarawa, Alhaji Kabir Tijjani Hashim a matsayin sabon Wamban Kano da Hakimin Gwale, Alhaji Mahmud Ado Bayero, a matsayin Turakin Kano.

Sai kuma Adam Lamido Sanusi da aka naɗa a matsayin Tafidan Kano da Alhaji Ahmad Abbas Sanusi a matsayin Yariman Kano.

Nasihar da Sanusi II ya yi wa sarakan

Yayin bikin nadin sarautar da aka gudanar a Fadar Sarkin Kano ranar Juma’a, Sanusi II ya bukaci waɗanda aka naɗa sarauta da su zama shugabanni nagari, masu sadaukarwa, da jin ƙai ga al’umma.

“An zaɓe ku ne bisa tarihin gudummawar da kuka bayar da na iyalanku. Da dama daga cikinku sun nuna ƙwazo da biyayya ga masarauta da danginmu.
"Kun taka rawa wajen taimakon talakawa da cigaban al’umma. Ina roƙon Allah ya ba ku ikon sauke nauyin da ke kanku.”

- Muhammadu Sanusi II.

Bikin naɗin ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf, mambobin majalisar zartarwa ta jihar, sarakuna da shugabannin addini, ‘yan uwa da abokan arziƙi.

Sanusi II.
An sake shiga ruɗani a Kano kan naɗin sabon Galadima Hoto: @MasarautarKano
Asali: Twitter

Aminu Ado ya naɗa Galadima a fadarsa

A ɗaya bangaren, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya nada kuma ya ɗora rawanin Alhaji Sunusi Lamido Ado Bayero a matsayin Galadiman Kano a fadar Nasarawa.

Wannan dai ya haifar da ruɗani game da sarautar Galadiman Kano, wacce take da ƙima da daraja a masarautar jihar.

Rashin Galadiman Kano

A watan Afrilu 2025, masarautar Kano ta yi babban rashi bayan rasuwar Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu rike da sarauta a jihar.

Rasuwarsa ta jefa al'umma cikin alhini, inda aka samu rarrabuwar kawuna wajen kai gaisuwar ta'aziyya ga sarakunan biyu masu iƙirarin sarauta a Kano: Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Bayan rasuwar Galadima, an samu sabani a cikin masarautar, inda kowanne daga cikin sarakunan biyu ya nada sabon Galadima.

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, yayin da Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15, ya naɗa Sanusi Ado Bayero a matsayin Galadima.

Wannan nadin biyu ya ƙara dagula al'amura a masarautar, inda aka samu jibge jami'an tsaro a harabar gidan Galadiman Kano da ke unguwar Galadanci domin tabbatar da tsaro yayin nadin sarautar.

Rikicin nadin Galadima ya nuna yadda rikicin sarauta a Kano ke ci gaba da haifar da rashin tabbas da kuma barazanar zaman lafiya a jihar.

Al'umma na fatan samun mafita mai dorewa daga hukumomi da masu ruwa da tsaki domin dawo da zaman lafiya da daidaito a masarautar Kano.

Jami'an tsaro sun mamaye gidan Galadima

A wani labarin, kun ji cewa tun a daren Juma'a, dakarun tsaro suka kewaye gidan Galadiman Kano da ke Unguwar Galadanci a ƙaramar hukumar Gwale.

An ruwaito cewa tun a jiya da daddare dakarun ƴan sanda suka jagoranci rufe gidan yayin da Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ke shirin naɗa Galadima biyu.

Jami'an tsaro sun ɗauki wannan matakin ne domin dakile duk wata tashin-tashina da ka iya faruwa a Kano kan naɗin sabon Galadima.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »