An Jibge Jami'an Tsaro yayin da Sanusi da Aminu ke Naɗa Galadima 2 a Kano
- Tun daga daren Juma'a, jami’an tsaro su ka mamaye kofar gidan Galadiman Kano da ke unguwar Galadanci, yayin da ake shirin nadin sabon Galadima
- Wannan na zuwa ne a lokacin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ke nada Munir Sanusi a matsayin sabon Galadima bayan rasuwar Abbas Sanusi
- Haka kuma Sakataren yada labaran fadar Nasarawa ya tabbatar da cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yana nada Sanusi Ado Bayero kan sarautar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – An wayi gari da ganin jami'an tsaro a harabar gidan Galadiman Kano da ke unguwar Galadanci, a karamar hukumar Gwale, yayin da ake gudanar da nadin sabon Galadima a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa tun cikin daren jiya Alhamis ne jami’an ‘yan sanda suka rufe kofar gidan Galadima gaba daya.

Asali: UGC
A wata zantawa da Legit, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, Sakataren labarai na fadar Nasarawa a karkashin Sarkin Kano na 15, ya tabbatar da cewa a yau ne za a nada sabon Galadiman Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Nadin na zuwa ne bayan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ayyana Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, bayan rasuwar Alhaji Abbas Sanusi.
Muhammadu Sanusi II ya zabi Munir Sanusi Bayero wanda shi ne Wamban Kano, ya gaji sarautar Marigayi Alhaji Abbas Sanusi.
Sarki Sanusi na nadin Galadiman Kano
A wani bidiyo da Abba Attijjani ya wallafa a shafinsa na Facebook, an hango yadda ake gudanar da taron nadin sabon Galadiman Kano, Munir Sanusi Bayero.
Wani dan jarida daga masarautar Kano ya shaidawa Legit.ng cewa ana sa ran yau ne Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai raka sabon Galadima zuwa gidan sarautarsa da ke Galadanci.

Asali: UGC
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a harabar gidan Galadiman Kano, inda aka takaita shiga da fita.
Sarkin Kano na 15 ya nada Galadiman Kano
A wani bidiyo da masarautar Kano ta wallafa a shafin Facebook, an hango jama’a suna kai gaisuwa ga sabon Galadiman Kano, Sanusi Ado Bayero.
A wasu sauran bidiyoyi da aka wallafa a shafin, an hango wasu hakimai da masu rike da sarautun gargajiya suna mika caffa ga Sarkin Kano na 15.
An jibge jami'an tsaro a Kano
Wani dan jarida mazaunin Kano, Abubakar Haruna Galadanchi ya shaidawa Legit cewa tun daren Juma'a aka jibge motocin jami'an tsaro da akalla suka kai guda 12.
Ya ce:
"Babu wata fargaba da muka ji, ai a cikin hari mun saba ganin motocin 'yan sanda."
Rikicin sarautar Kano
A cikin shekarun baya-bayan nan, masarautar Kano ta fuskanci rikice-rikice masu tsanani da suka shafi nadin sarauta da kuma shugabancin masarauta.
A shekarar 2020, gwamnatin Abdullahi Ganduje ta tsige Muhammadu Sanusi II daga mukamin Sarkin Kano bisa zargin rashin biyayya, inda ta raba masarautar Kano zuwa guda biyar tare da nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarki.
Sai dai, a watan Mayu 2024, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta soke dokar da ta kafa sabbin masarautun, tare da mayar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.
Wannan mataki ya haifar da sabani tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero, inda kowanne ke ikirarin zama halastaccen sarki.
Sanusi II yana zaune a fadar Kofar Kudu, yayin da Ado Bayero ke zaune a fadar Nasarawa tare da kariyar jami'an tsaro na gwamnati.
Haka kuma, kotuna sun bayar da umarni masu karo da juna dangane da halaccin nadin sarauta, lamarin da ya kara dagula al'amura a jihar.
A ranar 2 ga Mayu 2025, an samu karin rikici yayin da Sanusi II da Ado Bayero suka nada mutane daban-daban a matsayin Galadiman Kano.
Sanusi II ya nada Munir Sanusi Bayero, yayin da Ado Bayero ya nada Sanusi Ado Bayero. Wannan ya sa aka jibge jami'an tsaro a harabar gidan Galadiman Kano da ke unguwar Galadanci, domin tabbatar da tsaro yayin nadin sarautar.
Rikicin masarautar Kano na ci gaba da haifar da rashin tabbas da kuma barazanar zaman lafiya a jihar, inda al'ummar Kano ke fatan samun mafita mai dorewa daga hukumomi da masu ruwa da tsaki.
Sarkin Kano ya yi babban rashi
A baya, mun ruwaito cewa cewa a cikin alhini da jimami, masarautar Kano ta sanar da rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda ya rasu yana da shekaru 92 a duniya.
Galadiman, wanda shi ne babban jigon majalisar sarakunan Kano da ke taka muhimmiyar rawa a fada, ya koma ga Mahaliccinsa a ranar 1 ga Afrilu, 2025, bayan fama da rashin lafiya mai tsawo.
An gudanar da sallar jana’izar marigayin a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, da misalin karfe 10 na safe a ranar Laraba, 2 ga Afrilu, 2025, wanda manyan yan siyasa suka halartar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng