APC ko PDP: Shugaban EFCC Ya Fadi 'Yan Jam'iyyar da Hukumar Ta Fi Bincika

APC ko PDP: Shugaban EFCC Ya Fadi 'Yan Jam'iyyar da Hukumar Ta Fi Bincika

  • Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan zargin muzgunawa ƴan adawa
  • Ola Olukoyede ya bayyana cewa hukumar ta fi bincikar ƴan jam'iyya mai mulki saɓanin jita-jitar da ke cewa ana hantarar ƴan adawa
  • Olukoyede wanda ya shiga ofis a 2023 ya nuna ba rashin adalci ba ne a ƙi bincikar ƴan adawa saboda tsoron abin da masu suka za su ce

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar za ta binciki duk wanda ake zargi da aikata laifin keta doka, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da ya fito ba.

Ola Olukoyede ya musanta zargin cewa hukumar da nuna son kai ga jam’iyyar da ke mulki.

Shugaban hukumar EFCC
Shugaban EFCC ya ce ba su muzgunawa 'yan adawa Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Facebook

Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Laraba, 30 ga watan Afirilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

EFCC ta yi magana kan ayyukanta

Ya ce EFCC tana aiki ne bisa tsarin doka don tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi, ba tare da la'akari da jam’iyyar da ya ke ciki.

“Idan mun gano cewa ka wawure kudin jama’a, dole ka ba da bayani, ko da kai ɗan APC ne, PDP, LP, NNPP ko SDP."
“Don haka, komai jam’iyyar da kake ciki, aikinmu ne mu tabbatar mun yi abin da ya dace."
"Mu a wajenmu abin da muka damu da shi ne shin akwai laifin da ake zarginka da aikatawa? Mun gano wata matsala da dole ka yi bayani a kanta? Wannan shi ne abin da ke jan hankalinmu."

- Ola Olukoyede

Da yake ci gaba da magana kan zargin cewa hukumar na gallazawa ƴan adawa, Olukoyede ya ce an gurfanar da mambobin jam’iyyar APC, fiye da na jam’iyyun adawa.

“Idan ka duba ƙididdigar ayyukanmu a ɓangaren bincike da gurfanarwa musamman na manyan laifuka, za ka ga cewa yawan mambobin jam’iyyar da ke mulki muka gurfanar. Don haka a riƙa yi mana adalci."

- Ola Olukoyede

Ola Olukoyede
Shugaban EFCC ya ce an fi bincikar 'yan jam'iyya mai mulki Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Facebook

Su wa hukumar EFCC ta fi bincika?

A cewarsa, rashin binciken mambobin jam’iyyun adawa saboda tsoron abin da masu suka za su faɗa, babban rashin adalci ne.

“Za ka ga fitattun mambobin jam’iyyar da ke mulki cikin jerin waɗanda muka bincika kuma muka shigar da ƙara a kansu."
"Saboda haka, idan muka rufe ido ga waɗanda ba mambobin jam’iyya mai mulki ba, hakan ba zai zama adalci a gare mu ba, kuma zai nuna rashin gaskiya."

- Ola Olukoyede

EFCC ta cafke Akanta Janar na Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) sun cafke Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Jaja.

Jami'an na hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci sun cafke Sirajo Jaja ne a birnin Abuja bisa badaƙalar N70bn.

An cafke Sirajo Jaja ne tare da wasu mutum biyu bisa zargin safarar kuɗaɗe, karkatar da kuɗaɗen jama'a a madadin gwamnatin jihar Bauchi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »