Emefiele Ya Roki Kotu Ta Mallaka Masa Gidaje a Abuja, Alkali Ya Yi Fatali da Bukatar
- Babbar kotun tarayya a Abuja, ya yi watsi da bukatar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele
- Tsohon gwamnan bankin na neman a ba shi damar kalubalantar umarnin kwace rukunin gidaje 753 da ke Lokogoma a Abuja
- Gwamnatin tarayya, ta hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta samu umarnin kotu na kwace tulin kadarorin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mai shari’a Jude Onwuegbuzie na Babban Kotun Abuja, ya yi watsi da bukatar tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Mista Emefiele ya na neman kotun ta kwato rukunin gidaje 753 da dakunan haya a birnin tarayya daga hannun gwamnatin tarayya, ta mallaka masa.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa rukunin gidajen da ke Plot 109, Cadastral Zone CO9, Lokogoma District, ya mamaye fili mai fadin murabba’in mita 150,462.84.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Yadda aka kwace rukunin gidaje a Abuja
BBC Hausa ta kara da cewa an samu umarnin karbe rukunin gidajen gaba daya ne ta hannun Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a madadin gwamnatin tarayya.
An kwato rukunin gidajen a hannun wani tsohon babban jami’in gwamnati da ba a bayyana sunansa ba.
Sai dai Godwin Emefiele, ta bakin lauya A.M. Kotoye (SAN), ya shigar da bukatar kara wa’adin lokaci domin kalubalantar umarnin kwace kadarorin.
Emefiele ya kalubalanci kwace gidaje a Abuja
Emefiele ya ce bai san da zaman umarnin kotu ba, yana zargin cewa EFCC ta wallafa sanarwar wucin gadi ta kwace kadarorin ne a wani sashe da ba a cika dubawa ba a wata jarida.

Asali: Twitter
Ya kara da cewa a lokacin da aka fitar da sanarwar, yana fuskantar shari’a a kotuna daban-daban guda uku a Abuja da Legas, wanda hakan ya hana shi gano sanarwar cikin lokaci.
Emefiele ya zargi EFCC da boye masa batun kwace kadarorin duk da cewa suna ci gaba da mu’amala da shi a wasu tuhuma daban.
Kotu ta yi watsi da bukatun Emefiele
A hukuncinsa, Mai shari’a Onwuegbuzie ya ce ikirarin Emefiele cewa sanarwar ba ta bayyana ba, ba ta da tushe, yana mai cewa:
"Sanarwar da ta shafi rabin shafi a jaridar kasa ba za a ce an ɓoye ta ba."
Alkalin ya yanke hukuncin cewa Emefiele ya wuce wa’adin kwanaki 14 da doka ta tanada domin kalubalantar kwace kadarorin, amma bai dauki mataki ba.
Buhari, Emefiele sun yi nasara a kotu
A wani labarin, kun ji yadda kotu ta yi watsi da karar da wani Uthman Isa Tochukwu ya shigar kan Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Lauyan, Tochukwu ya kai su kara ne yana zargin cewa tsarin sauya takardar Naira da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi, ya jefa shi cikin wahalhalu masu yawa.
Ya kara da cewa a lokacin da gwamnatin Buhari ta aiwatar da tsarin sauya Naira tsakanin Janairu da Maris, 2023, ya shiga cikin mummunan hali da rashin iya cirar kudi daga bankuna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng