Tsofaffin Shugabanni 5 a Zamanin Buhari da EFCC ke Bincike a Gwamnatin Tinubu

Tsofaffin Shugabanni 5 a Zamanin Buhari da EFCC ke Bincike a Gwamnatin Tinubu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta fara binciken wasu tsofaffin shugabannin Najeriya da suka yi aiki tsakanin 2015 zuwa 2023.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugabannin, wadanda suka yi a mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, na fuskantar tuhuma da laifukan cin hanci da rashawa.

Zargi
EFCC na tuhumar tsofaffin jagorori a gwamnatin Buhari Hoto: NNPC Limited/Alhaji Yahaya Bello/Ifeanyi Arthur Okowa
Asali: Facebook

Legit ya tattaro wasu tsofaffin shugabanni biyar da hukumar EFCC ke zargi da laifuffukan tattara kudin kasa, suka zuba a aljihunsu.

1. EFCC da Yahaya Bello (2016–2024)

Jaridar The Cable ta wallafa cewa a watan Afrilu 2024, EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu bisa zargin almundahana da kuɗin gwamnati har Naira biliyan 80.2.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

An tuhume shi da laifuffukan da suka shafi halasta kuɗin haram da karkatar da kuɗin gwamnati.

Har yanzu ana ci gaba da shari'ar da shi, duk da yunkurin da ya yi a baya na gujewa kamun EFCC ko zuwa kotu.

2. Zargin da EFCC ke yiwa Ifeanyi Okowa

Channels TV ta ruwaito cewa a watan Nuwamba 2024, EFCC ta gayyaci Ifeanyi Okowa bisa zargin karkatar da Naira tiriliyan 1.3 domin amfanin kashin kai.

Ola Olukoyede
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

An kuma tuhume shi da amfani da Naira biliyan 40 wajen sayen hannun jari a kamfanin LNG ba tare da bin ka'idoji ba.

Hakanan, EFCC na bincikensa kan mallakar kadarori a Abuja da Asaba da ake zargin an saya da kudaden gwamnati.​

3. EFCC na shari'a da Godwin Emefiele

Tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele na fuskantar tuhuma daga EFCC kan laifuffukan da suka da amfani da kujerarsa wajen amfana da kuɗin gwamnati.

An tuhume shi da laifukan da suka shafi buga sababbin takardun kuɗi ba tare da izini ba da kuma cire kuɗin gwamnati ba bisa ka'ida ba.​

4. Zargin EFCC a kan tsohon shugaban NHIS

EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf bisa zargin almundahana da kuɗin hukumar NHIS.

An tuhume shi da laifuffukan da suka hada da bayar da kwangiloli ba bisa ka'ida ba da kuma amfani da matsayinsa wajen amfana da kansa.​

Duk da kama shi da jami'an tsaro suka sha yi, Farfesa Usman wanda ya fara aiki tsakanin 2016-2019 ya ce gwamnati na yi masa bita da ƙulli me saboda adawa da ita.

5. EFCC za ta tuhumi Mele Kyari

Mele Kyari, wanda ya bar aikin shugabancin NNPCL a kwanan nan zai iya fara fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC.

Tun bayan da ya kammala aikinsa a EFCC ne aka rika kai koke ga hukumar EFCC da ta gaggauta daukar mataki da fara bincike a kansa.

Hukumar ta bakin kakakinta, Dele Oyewale ya ce EFCC za ta yi a abin da ya dace don fara tuhumar Mele Kyari bisa koken jama'a.

Daga cikin laifuffukan da ake son tuhumarsa da su akwai bayar da kwangiloli ba bisa ka'ida ba, da amfani da matsayinsa wajen amfanar da kansa.​

Ana son haɗa Mele Kyari da EFCC

A baya, kun samu labarin cewa kungiyoyin fararen hula sun bukaci hukumar EFCC ta fara bincike a kan tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari kan wasu kuɗi $1.5bn.

Ƙungiyar ta bayyana wannan bukata ne yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja, inda ta ce dole ne a zakulo gaskiyar yadda aka kashe makudan kuɗin.

Jagoran ƙungiyar, Michael Omoba, ya yaba da matakin Shugaba Bola Tinubu na sauke Kyari daga mukaminsa, yana mai cewa hakan zai tsaftace harkokin man fetur.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »