Nuhu Ribadu Ya Fadi Dalilin Lalacewar Tsaro a Gwamnatinsu
- Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi takaicin kashe kashe da suka karu a kasar nan
- Ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta tarar da Najeriya cikin wani mawuyacin hali, wanda ya kara dagula matsalar
- A ziyarar da ya kai Binuwai, Ribadu ya ce gwamnatin tarayya ta jajirce wajen shawo kan yawan kashe-kashe a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa
Jihar Benue – Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin shugaban kasa, Bola Tinubu ta gaji tsananin matsalar tsaro daga gwamnatin baya.
Duk da haka, Ribadu ya ce gwamnatinsu ta na kokari ba dare ba rana domin dawo da zaman lafiya a sassan kasar nan da ke fama da rashin zaman lafiya da kashe-kashe.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Ribadu ya bayyana haka ne yayin wani taron tsaro da aka gudanar tare da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin jihar Binuwai da ke Makurdi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Nuhu Ribadu ya yi ta’aziyya ga mutanen Binuwai
Daily Post ta ruwaito cewa Nuhu Ribadu ya yi ta’aziyya ga al’ummar jihar Binuwai bisa yawan kashe-kashen da kuma hare-haren a jihar.
Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tukuru har sai an shawo kan lamarin.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Za mu shawo kan wannan matsala. Najeriya na tare da ku.”
“Ina jajanta wa mutanen Binuwai, kuma ina tabbatar muku da cewa wannan lokaci ne mai wahala gare mu gaba ɗaya, amma muna tare da ku dari bisa dari.”
Binuwai na da muhimmanci ga Najeriya – Ribadu
Ribadu ya jaddada cewa Binuwai na da matukar muhimmanci a tsarin tsaron Najeriya, don haka gwamnati za ta kara himma wajen ganin an samu dawwamammen zaman lafiya a yankin.
A cewarsa:
“Binuwai jiha ce mai matukar muhimmanci a Najeriya. Dole ne mu kare ta mu tabbatar da zaman lafiya.”
Ya kuma yabawa gwamnan jihar, yana mai cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da goyon bayan sa.
‘Jami’an tsaro na kokari’ Inji Ribadu
Ribadu ya bayyana cewa dakarun tsaron Najeriya na kokari, amma ya ce ba zai yiwu a tura sojoji ko ‘yan sanda zuwa kowane kauye ba.
Ya ce:
“Sojojinmu da jami’an tsaro na kokari. Ba zai yiwu mu tura su kowane lungu da saƙo ba. Abin da muke bukata shi ne hadin kai daga jama’a da kuma a daina siyasantar da kashe-kashen. Wannan ne zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya.”
Nuhu Ribadu ya kara da cewa gwamnatin Tinubu ta fara ganin ci gaba a kokarin da take yi wajen dakile matsalolin tsaro, duk da irin halin da ta gada daga gwamnatin baya.
An sace motar ofishin Nuhu Ribadu
A baya, mun wallafa cewa rundunar 'yan sanda reshen birnin tarayya ta fara bincike kan sace wata mota da aka yi a harabar wani masallacin Juma’a a Abuja.
Wannan ya biyo bayan zargin wasu da satar motar jami’in ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a garin Abuja.
Kwamishinan 'yan sanda ya ce za su bi duk wata hanya da za ta kai ga gano motar da kuma masu hannu a satar domin a hukunta su daidai da laifinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng