
Latest







Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tanadi hukunci kan shari'o'in da ke neman tsige gwamnan Edo. PDP na kalubalantar nasarar APC, inda ta ce akwai kuskure a zaben.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace basarakena jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, ƴan sanda sun fara farautarsu domin ceto shi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya yi magana kan zaben 2027 da ake shirin kifar da Bola Tinubu inda ya ce har da jam'iyyar APC.

Rikici tsakanin manoma da makiyaya a Nangere, Yobe ya yi sanadin mutuwar mutum daya da jikkatar wasu da dama, an kwato dabbobi 31 yayin da bincike ke ci gaba.

Bayan harin yan bindiga a Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya tabbatar da mutuwar ‘yan bindiga fiye da 60 a harin da ya faru a kauyen Mansur na karamar hukumar Alkaleri.

'Yan sanda sun kama Fatima Salisu a Nasarawa da harsasai 481, ana zargin tana safarar su ga ’yan ta’adda a Katsina. Yanzu haka dai ana ci gaba da bincikarta.

Jama'a da dama sun rasa muhallansu yayin da aka yi wata guguwa mai ƙarfi haɗe da ruwan sama a wasu sassan jihar Katsina, ciki har da wasu sababbin ma'aurata.

An samu barkewar rikicin manoma da makiyaya a wasu kauyukan jihar Taraba. Rikcin ya jawo an samu asarar rayukan mutane daga bangaren manoma da makiyaya.

Primate Ayodele ya hango rikice-rikicen da za su fada wa gwamnonin jihohi 6, inda ya bukace su da su guji siyasar rikici, su mayar da hankali kan jin daɗin jama'a.
Masu zafi
Samu kari