'Domin Cusa Aƙidar Musulunci': Dattijo a Kannywood Ya Fadi Dalilin Shiga Fim

'Domin Cusa Aƙidar Musulunci': Dattijo a Kannywood Ya Fadi Dalilin Shiga Fim

  • Fitaccen jarumi a Kannywood, Malam Inuwa Ilyasu, ya bayyana cewa ya shiga harkar fim ne domin fadakar da jama'a da kuma koyar da addinin Musulunci
  • A cewar Malam Inuwa, bai zabi fitowa a matsayin malami a fina-finai ba, sa'a ce kawai ta sa yana samun waɗannan ɓangare wanda kuma yana jin dadin haka
  • Ya ce masana'antar fim ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan matasa, musamman wurin koyar da ɗabi'a, tarbiyya da kuma al'adar Hausawa
  • Malam Inuwa wanda ya shafe fiye da shekaru 40 yana harkar, ya ce da su aka fara fim tun daga wasan daɓe kafin ci gaban masana'antar zuwa yanzu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Fitaccen dattijo a masana'antar Kannywood, Malam Inuwa Ilyasu ya fadi dalilin shigarsa sana'ar.

Jarumin Kannywood ya ce ya shiga harkar masana'antar ne domin fadakarwa da koyar da addinin Musulunci da kuma cusa aƙida.

Jarumin fim ya fadi dalilin shigarsa sana'ar fim
Jarumi kuma dattijo a Kannywood, Malam Inuwa Ilyasu ya ce ya shiga fim domin fadakarwar addinin Musulunci. Hoto: Fagen Kannywood.
Asali: Facebook

Jarumi ya fadi dalilin shiga harkar fim

Malam Inuwa Ilyasu wanda ke yawan fitowa a matsayin malami ya fadi haka ne yayin hira ta musamman da jaridar Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Yayin hirar, Malam Inuwa ya ce ba wai zaben abin ya da yake son zama a fim yake ba, sa'a kawai yake yi da dace.

Ya bayyana irin gudunmawar da harkar fim ta bayar wurin fadakarwa da kuma koyan darusa ga al'umma.

A hirar, ya ce:

"Yauwa, ana yin sa’a ce dai za ni ce ta tarar da mu je, domin ni daman dalilina na yin wasan kwaikwayo shi ne, saboda in samu in cusa aƙida ta addinin Musulunci da tarbiyartarwarsa.
"Da kuma cusa al’adarmu da ɗabi’unmu ga matasa masu tasowa.
"Misali, ai ka ga irin yadda wasu masu fim ɗin Indiya suke cin karensu babu babbaka"

Jarumin Kannywood ya fadi dalilin fara sana'ar fim
Jarumi kuma dattijo a Kannywood ya ce ya shiga fim domin koyar da Musulunci. Hoto: Fagen Kannywood.
Asali: Facebook

Shekarun jarumin fim, Inuwa a Kannywood

Jarumin wanda ya shafe shekaru 40 yana fim ya ce kusan da su aka fara harkar tun lokacin daɓe kafin samun ci gaba zuwa yanzu.

Ya kuma tabo batun rigingimu da ake samu tsakanin jarumai ko mawaka inda ya ce hakan dan Adam yake dole a samu sabani.

"Gaskiya dai kusan da ni aka fara yin fim kuma lokacin da muka fara yi, mun fara da yin tunanin ya za mu yi saboda kafin nan ai akwai wasan daɓe da muka fara yi."

Sadik ya fadi dalilin shigarsa sana'ar fim

A wani labarin mai kama da wannan, mun ruwaito cewa jarumin Kannywood, Sadik Sani Sadik ya ce ya na harkar fim ne ba don koyar da tarbiyya ba, sai domin neman kuɗi kawai.

Matashin 'dan wasan kwaikwayon ya ce tarbiyya daga gida take fitowa yayin da ya ce malamai ke fadakarwa, ba 'yan fim ba kamar yadda wasu ke zato.

Sadik Sani Sadik ya jaddada cewa idan fim dinsa ya shafi tarbiyya, laifin iyaye ne ba nasa ba saboda nauyi na kansu haka ma idan ya gyara musu an yi dace ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »