Kotu Ta Yi Hukunci kan Bukatar Firaministan Isra'ila bayan Kammala Yaƙi da Ƙasar Iran
- Firaministan Isra'ila, Benjamim Netanyahu ya yi rashin nasara a ƙoƙarinsa na dakatar da shari'ar da ake masa kan tuhumar karɓar rashawa
- Kotun da ke kasar Isra'ila ta yi fatali da buƙatar Netanyahu a hukuncin da ta fitar yau Juma'a, tana mai cewa babu wata hujja mai ƙwari
- Tun farko Lauyan Netanyahu ya bukaci ɗage shari'ar ne saboda a bar Firaministan ya maida hankali kan batun tsaro bayan gama yaki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Isra'ila - Wata kotu a Isra’ila, a ranar Juma’a ta ƙi amincewa da buƙatar Firaminista, Benjamin Netanyahu na jinkirta gurfanar da shi kan zargin rashawa.
A jiya Alhamis, Lauyan Netanyahu ya roƙi kotun ta dakatar da zaman shari’ar da aka shirya nan da makonni biyu.

Asali: Getty Images
Lauyan ya kafa hujja da cewa shugaban na bukatar mai da hankali kan “batutuwan tsaro” bayan yaƙin kwanaki 12 da Isra’ila ta yi da Iran, in ji rahoton Arab English.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Wane hukunci kotu ta yi kan bukatar Netanyahu?
Sai dai yayin da take yanke hukunci kan wannan buƙata a yau Juma'a, kotun da ke zama yankin birnin Jerusalem ta ce:
“A yadda buƙatar ta ke yanzu, ba ta ƙunshe da wata hujja mai ƙarfi ko cikakken bayani da zai sa a soke zaman shari’ar da aka shirya.”
A ranar Laraba da ta shige, shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana shari’ar da ake wa Netanyahu a matsayin “farauta” yana mai cewa ya kamata a soke ta ko a yi masa afuwa.
Netanyahu ya nuna godiyarsa ga Trump bisa goyon bayan da ya bashi a lokacin yaƙin Isra’ila da Iran, wanda ya ƙare da yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 24 ga Yuni.
Netanyahu ya musanta zargin karɓar rashawa
Firaministan na Isra'ila ya kuma musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yayin da magoya bayansa ke ganin cewa shari’ar tuggun siyasa ce aka kitsa.
A karar farko, an zarge shi da matarsa Sara Netanyahu da karɓar kayayyaki da suka kai darajar $260, 000, ciki har da sigari mai tsada, kayan ado da giya daga wasu attajirai da sunan alfarmar siyasa.
A zaman shari'a guda biyu da aka yi, an ce Netanyahu ya yi ƙoƙarin shawo kan wasu kafafen yaɗa labarai a Isra’ila don su riƙa wallafa labaran kirki a kansa, rahoton The Times of Israel.

Asali: Getty Images
Yadda Netanyahu ya fara gyara tsarin shari'a
Tun da ya sake zama Firaminista a ƙarshen 2022, gwamnatisa ta fara gyare-gyaren tsarin shari’a, wanda ƴan adawa suke zargin an tsara su ne don rage ƙarfin ikon kotuna.
Netanyahu ya sha nema a dage shari’ar tun lokacin da aka fara ta a watan Mayu 2020, yana amfani da dalilan yaƙin da yake yi a Gaza a 2023, daga baya a Lebanon, da kuma rikicin kwanan nan da Iran.
Isra'ila ta yi niyyar kashe jagoran addinin Iran
A wani labarin, kun ji cewa ƙasar Isra'ila ta bayyana cewa ta yi niyyar kashe Jagoran Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz ne ya sanar da hakan bayan shafe kwanaki 12 ana musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu.
Katz ya bayyana cewa Khamenei ya fahimci rayuwarsa na cikin hadari, wanda hakan ya sa ya buya a karkashin kasa domin tsira da rai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng