Isra'ila Ta Fadi Yadda Ta Shirya Kashe Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Khamenei
- Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya ce kasarsa ba ta bukatar izini daga Amurka don kaddamar da harin da zai kashe jagoran Iran
- Ya bayyana haka ne a lokacin da aka kawo karshen yakin da aka rika fargabar zai iya mamaye dukkanin Gabas ta Tsakiya
- A cewar Ministan tsaron, ba umarnin Amurka ne ya hana kasarsa kashe Ayatollah Khamanei da ke jagorantar Shia'a a duniya ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Isra'ila – Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana cewa kasarsa ta yi niyyar kashe Jagoran Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Yana wannan bayani ne bayan an kammala yakin kwanaki 12 a tsakanin kasashen biyu da kowacce ke ikirarin ita ce ta yi nasara.

Asali: Getty Images
Aljazeera ta wallafa cewa Katz ya ce Isra’ila ba ta bukatar amincewar Amurka don kaddamar da harin kashe Khamenei.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Isra’ila ta yi yunkurin kashe jagoran Iran
Jaridar The Times of Israel ta ruwaito cewa Katz ya bayyana cewa Khamenei ya fahimci rayuwarsa na cikin hadari, wanda hakan ya sa ya buya a karkashin kasa domin tsira da rai.
Katz ya ce jagoran addini na Iran ya katse hulda da wasu daga cikin manyan kwamandojin da suka maye gurbin shugabannin dakarun IRGC da Isra’ila ta kashe a harin farko.
Ya ce:
“Mun so mu kashe Khamenei, amma ba a samu damar aiwatar da hakan ba.”
Sai dai ba a da wata hujja da ta tabbatar da cewa Khamenei ya yanke hulda da kwamandojinsa ba, domin kuwa yana ci gaba da fitar da sakonnin bidiyo a lokacin yaki.
Illar yunkurin Isra’ila kan Khamenei
Rahotanni sun nuna cewa da an yi sa'ar kashe Ayatollah Khamenei, lamarin zai haifar da mummunar tabarbarewar rikicin Iran da Isra’ila.
Ayatollah ba wai shugaban Iran ne kawai ba, har ila yau shi ne jagoran miliyoyin Musulmi ‘yan Shi’a a duniya.

Asali: Getty Images
A baya, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, sun nuna cewa yaki tsakanin Iran da Isra’ila na iya haifar da sauyin gwamnati a Iran.
A yakin da aka gwabza, rahotanni sun ce Amurka ce ta fi haddasa barnar a cibiyoyin nukiliya na Fordow, Natanz da Isfahan ta hanyar jefa bama-bamai.
Kuma Ministan tsaron Isra’ila ya ce kasar sa ta samu sahalewa daga Trump don sake kai hari idan an ga Iran na ci gaba da shirin nukiliyarta.
Katz ya kara da cewa:
“Ba na ganin Iran za ta iya farfado da wuraren nukiliyarta bayan harin.”
Iran ta kashe yan leken asirin Isra'ila
A wani labarin, mun wallafa cewa hukumomin Iran sun gudanar da kame tare da zartar da hukuncin kisa ga wasu da ake zargi da aikata leken asiri domin kasar Isra’ila.
Wannan na daga cikin wani mataki da ke nuna tsauraran matakan tsaron da kasar ke dauka bayan rikicin kwanaki 12 da suka yi da Isra’ila, inda mutane da dama suka rasu.
Wannan na zuwa ne bayan da jami’an Iran sun bayyana cewa Isra’ila ta kutsa cikin hukumomin tsaro na kasar a wani abin da suka kira kutsawa mafi muni da aka taba gani a tarihi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng