Yaki Ya Kare: Iran Ta Sanar da Kawo Karshen Musayar Wuta da Israila

Yaki Ya Kare: Iran Ta Sanar da Kawo Karshen Musayar Wuta da Israila

  • Ƙasashen Iran da Israila sun kwashe kwanaki 12 suna musayar wuta bayan yaƙi ya ɓarke a tsakaninsu
  • Shugaban ƙasar Iran ya sanar da cewa yaƙin na kwanaki 12 ya zo ƙarshe bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Masoud Pezeshkian ya nuna cewa Iran ta nuna jarumta a yaƙin wanda Israila ta ƙaƙaba mata bayan ta fara kai mata hari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Iran - Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi magana kan yaƙin da ƙasarsa ke yi da Isra'ila.

Shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa 'yaƙin kwanaki 12' da Iran ke yi da Isra’ila ya ƙare.

Yakin Israila da Iran ya zo karshe
Iran ta kawo karshen yakinta da Israila Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tashar Aljazeera ta rahoto cewa shugaban na Iran ya sanar da hakan ne a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin na gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Shugaban Iran ya ce yaƙi ya ƙare

Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa yaƙin na kwana 12 da Israila ta tilasta musu shiga ya zo ƙarshe.

“A yau, bayan jarumtar da ƙasar mu mai girma ta nuna, wacce jajircewarta ke kafa tarihi, muna sanar da daidaituwar zaman lafiya da kuma ƙarshen wannan yaƙin na kwanaki 12 da Isra’ila ta ɗora mana ta hanyar fitina da tada husuma."

- Masoud Pezeshkian

Hakazalika ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa Iran yanzu za ta ƙara ƙaimi wajen ci gaba da riƙe shirinta na nukiliya bayan wannan hare-hare da Isra’ila ta kai na kwanaki 12.

"Mun yi matuƙar ƙoƙari wajen mallakar wannan fasaha. Masananmu sun sadaukar da rayukansu, wasu har suka mutu domin cimma wannan buri."
“Mutanenmu sun jure wahalhalu saboda hakan, kuma aka ɗora wa ƙasarmu yaki saboda wannan batu. Abu ne tabbatacce cewa babu wani ɗan Iran da zai yarda a miƙa wannan fasaha."

- Abbas Aragchi

Netanyahu ya ce sun samu nasara kan Iran

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa ƙasarsa ta samu nasara a yaƙin da ta yi da Iran.

Iran da Israila sun yi yakin kwanaki 12
Israila ta ce ta yi nasara kan Iran Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images
"Mun samu nasara mai tarihi, kuma wannan nasara za ta dawwama har zuwa ga al’ummomi masu zuwa."
“Mun tashi tamkar zaki, kururuwar mu ta girgiza Tehran. Wannan yaƙi za a koyar da shi a dukkan makarantun soja na duniya. Mun lalata cibiyoyin fasaha masu muhimmanci da ke Arak, Natanz da Isfahan."
“Idan Iran ta ƙara yunƙurin gina shirinta na nukiliya, za mu lalata shi. Dole ne mu kammala wannan aiki na yaƙi da Iran da abokan hamayyarta ta hanyar ceto sojojin da aka sace da kuma kawar da Hamas."

- Benjamin Netanyahu

Haka kuma, jami’an Iran sun bayyana cewa su ma sun yi nasara a wannan yaƙi, inda suka jaddada cewa Isra’ila da Amurka ne suka roƙi a tsaida wuta, ba tare da sun cimma burinsu ba wato rushe shirin nukiliya da makaman masu linzami na Iran.

Iran ta faɗi mutanen da ta rasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Iran ta bayyana adadin ɓarnar da aka yi mata a yaƙin da ta yi da Israila.

Iran ta bayyana cewa ta rasa fararen hula mutum 610 a yaƙin da aka shafe kwanaki 12 ana yi tsakanin ƙasashen biyu.

Hakazalika ta ƙara da cewa wasu ƙarin mutum 4,100 sun samu raunuka daban-daban sakamakon yaƙin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »