Iran Ta Ƙara Yi Wa Isra'ila Mummunar Illa, Yahudawa Sama da 8,000 Sun Shiga Duhu
- Hare-haren da Iran ke ci gaba da kai wa ƙasar Isra'ila ya jawo ɗaukewar wutar lantarki a sassa daban-daban
- Rahotanni sun nuna cewa yahudawa sama da 8,000 na fama da matsanancin rashin wutar lantarki sakamakon harin Iran
- Ministan makamashi na Isra'ila ya ce sun yi tsammanin faruwar haka, kuma tuni suka fara ɗaukar matakan gyara wutar lantarki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tel Aviv, Israel - Rahotanni sun nuna cewa luguden wutar da ƙasar Iran ke ci gaba da yi wa yahudawa ya katse wutar lantarki a sassa daban-daban a Isra'ila.
Fiye da mutum 8,000 ne suka fuskanci matsanancin rashin wutar lantarki a wasu sassan Isra’ila bayan hare-haren da Iran ta kai a ƙasar.

Asali: Getty Images
Ministan Makamashi na Isra’ila, Eli Cohen, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda BBC Hausa ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Iran ta katse wutar lantarki a Isra'ila
A cewar Ministan, hukumomi sun riga sun shirya tun da farko don fuskantar irin wannan barazana, tare yana mai cewa za a maido da wutar a cikin awa uku.
Cohen ya tabbatar da cewa gwamnatin Isra'ila za ta gyara wuta domin rage wa jama’a radadin rashin hasken lantarki da sauran nau’o’in matsalolin yau da kullum.
"Mun yi tunanin da yiwuwar irin wannan hare-hare, don haka tun kafin haka mun tanadi matakan gaggawa domin dakile tasirinsu,” in ji Cohen.
'Yan Isra'ila na fama da rashin wutar lantarki
Hukumar Wutar Lantarki ta Isra’ila (IEC) ta tabbatar da cewa wasu muhimman gine-ginenta da ke kudancin Isra’ila sun lalace sakamakon hare-haren da Iran ta kai.
Ta ce wannan lamari ne ya haifar da ɗauke wutar lantarki gaba ɗaya a wasu yankuna a ƙasar Isra'ila.
“Wannan hari ya shafi wasu cibiyoyin wutar lantarkinmu, amma injiniyoyi sun riga sun fara aikin gyara domin tabbatar da dawo da wutar cikin gaggawa,” in ji IEC.
Hukumar ta ce wakilanta sun bazu zuwa yankunan da abin ya fi shafa, musamman a yankin Negev da kusa da Tekun Maliya, inda aka fi jin tasirin hare-haren.

Asali: Twitter
Gwamnatin Isra'ila ta sha alwashin kare jama'a
Hakan dai na cikin illolin da Iran ta yi wa Isra'ila a hare-haren da take ci gaba da kai wa yayin da musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari.
Duk da haka, Gwamnatin Isra’ila ta bayyana ƙarfin gwiwarta na ci gaba da kare duk wata barazana da za ta iya hana al’umma rayuwa cikin lumana.
Ta tabbatar da cewa an tanadi kayan gyara da ƙwararrun ma’aikata domin dawo da wutar lantarki ba tare da jinkiri ba, kamar yadda Al-Jazeera ta kawo.
Mutanen Isra'ila dai na ci gaba da fuskantar matsalar ababen more rayuwa tun faran ɓarkewar yaki tsakanin ƙasarsu da Iran.
Koriya ta Arewa ta caccaki Amurka da Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa Koriya ta Arewa ta nuna tsananin fushinta kan hare-haren da Amurka ta kai kan wasu cibiyoyin nukiliya a Iran.
Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta zargi Amurka da Isra’ila da haifar da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar karya dokokin ƙasa da ƙasa.
Iran da Koriya ta Arewa, wacce ke da makaman nukiliya, suna da dangantaka mai kyau tun shekaru da dama da suka gabata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng