Amurka Ta Kai Harin Farko Iran, Ta Jefa Bama Bamai a Manyan Wuraren Haɗa Nukiliya
- Amurka ta sanar da nasarar kai hari kan cibiyoyin nukiliya uku a Iran, ciki har da Fordo, da nufin lalata shirin nukiliyar kasar
- Hare-haren sune na farko kai tsaye daga Amurka kan Iran, inda suka haɗa da jefa bama-bamai masu yawa a babbar cibiyar Fordo
- An yi amfani da jiragen B-2 stealth bombers masu ɗaukar bama-baman GBU-57, waɗanda ke da ƙarfin kutsawa cikin cibiyoyin Iran
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar a shafin sada zumunta a ranar Asabar cewa, Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliya da dama a Iran.
Waɗannan hare-hare ta sama sune na farko da Amurka ta kai kai tsaye kan Iran, kuma sun ƙara rura wutar rikici tsakanin Iran da Isra'ila wanda ya fara a ranar 13 ga Yuni.

Asali: Getty Images
Amurka ta kai harin farko kan Iran
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X da karfe 12:53 na safiyar Lahadi, Trump ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
"Mun samu nasara a harin da muka kai kan cibiyoyin nukiliya guda uku a Iran, ciki har da Fordo, Natanz, da Esfahan.
"Dukkan jiragen da suka kaddamar da harin sun fice daga sararin samaniyar Iran. An jefa bama bamai masu yawa a babbar cibiyar nukiliyar Fordo. Dukkan jiragen suna kan hanyarsu ta dawowa gida lafiya."
Trump ya ƙara da cewa:
"Ina taya manyan jarumanmu na Amurka murna. Babu wani soji a duniya da zai iya yin haka. Yanzu lokaci ne na zaman lafiya! Na gode da damuwar da kuka nuna kan wannan lamari."
Dalilin hari kan cibiyar nukiliyar Fordo
Isra'ila ta iya kai hari kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran da kanta, amma an yi ammana cewa ba ta da karfin da za ta iya farmakar cibiyar nukiliyar Iran, watau Fordo.
Cibiyar nukiliyar Fordo, wacce ita ce mafi haɓaka da tarin Uranium a Iran, an gina ta ne a karkashin cikin dutse kuma ana tunanin tana da tsaro daga kowane irin bam.
Sai dai, bam daya ne yake iya zama barazana a gare ta, watau GBU-57 - MOP na Amurka, wani makami da ake yi wa lakabi da "bunker buster" a turance, inji rahoton NBC News.

Asali: UGC
Wanne bam Amurka ta harba wa Iran?
Trump bai faɗi irin bama-baman da aka yi amfani da su a hare-haren ba, amma ana tsammanin Amurka ta yi amfani da GBU-57 kan Fordo.
Tun a safiyar ranar, jiragen Amurka na B-2 stealth bombers, waɗanda sune kaɗai jiragen da za su iya ɗaukar bama-baman GBU-57 masu nauyin fam 30,000, su ka bar sansanoninsu da ke a Amurka.
Amurka ta samar wa Isra'ila ƙananan bama baman GBU-57 amma ba a san Isra'ila tana da jirgin da zai iya daukar bama baman ba, wanda hakan ya sa ake ganin duk harin da ya yi nasarar taba Fordo, to daga Amurka yake.
Karanta sanarwar Trump a nan kasa:
Iran ta mayar da martani bayan harin Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rikicin dake tsakanin Isra'ila da Iran ya ƙara tsananta bayan da Amurka ta kai harin bama-bamai kan cibiyoyin nukiliya uku a Iran.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Iran ta mayar da martani nan take, inda ta harba rokoki da bama-bamai kan wurare da dama a ƙasar Isra'ila.
Jami'an ceto sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka bayyana cewa hare-haren da Iran ta kai sun jikkata akalla mutane 11 kawo yanzu.
Asali: Legit.ng