Makamai 40 da Iran Ta Harba Sun Gamu da Cikas, An Kakkaɓo Su kafin Su Kai Isra'ila

Makamai 40 da Iran Ta Harba Sun Gamu da Cikas, An Kakkaɓo Su kafin Su Kai Isra'ila

  • Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa na bam da Iran ta harbo zuwa cikin ƙasarta
  • A wata sanarwa da sojojin suka fitar, sun ce kawo yanzu Iran ta harbo makamai sama da 470 amma duk kusan ta yi nasarar kakkaɓo su
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da yaƙi tsakanin kasashen biyu ke kara ta'azzara a rana ta takwas watau yau Asabar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tel Aviv, Israel - Ƙasar Iran ta sake harba jirage marasa matuƙa masu fashewa kamar bam zuwa Isra'ila, sai dai hukumomi sun ce sun tare su ba tare da matsala ba.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta na sama sun kakkaɓo kusan jiragen sama marasa matuki guda 40 da aka harbo daga Iran cikin dare.

Sojojin Isra'ila sun tare farmakin Iran.
Rundunar sojin sama ta Isra’ila ta ce ta Harbo kimanin jiragen yaki 40 daga Iran Hoto: @Iran
Asali: Twitter

A rahoton da Aljazeera ta kawo, rundunar ta yi ikirarin cewa ta samu nasara kusan kashi 99 cikin 100 na harbo irin waɗannan makaman tun da ta fara rikici da Iran.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Isra'ila ta yi ikirarin kakkabo makaman Iran

Wannan ikirari na rundunar sojin kasar Isra'ila na nuni da cewa mafi yawan makaman da Iran ta harbo, ba su kai ga wurin da aka nufi su ruguza ba.

A yau Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025 aka shiga rana ta takwas tun bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙasashen biyu a ranar Juma'a, 13 ga watan Yuni.

A cikin wata sanarwa, rundunar sojin ta ce:

“A daren jiya Juma'a, sojojin sama sun yi nasarar harbo kimanin jirage marasa matuki guda 40 da aka turo daga Iran zuwa cikin ƙasar Isra’ila.”
“Wannan adadi na makaman da aka harbo na ci gaba da ƙaruwa tun daga farkon ranar da aka fara musayar wuta

"A yanzu alƙaluma sun nuna Iran ta harbo makamai fiye da 470 kan Isra'ila, amma dai sojojin mu na sama sun kakkaɓo kashi 99 cikin 100 na jirage marasa matuƙa.”
Sojojin Isra'ila sun harbo jirage marasa matuƙa.
Sojojin Isra'ila sun kakkabo makamai 40 da Iran ta harbo Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Sojojin Isra'ila sun kai hari wasu wurare a Iran

Sanarwar ta kuma bayyana cewa jiragen yaƙi na musamman na Isra'ila ƙarƙashin jagorancin ɓangaren leƙen asiri, sun kai farmaki kan wata na’urar harba makamai ta Iran a birnin Isfahan.

Bugu da ƙari, rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa dakarunta suna kai farmaki kan cibiyoyin soji da ke Kudu maso Yammacin Iran.

Sojojin sun jaddada cewa za su ci gaba da ƙoƙarin kakkabo duk wani makamai ko jirgi da aka harbo, sannan ta maida martani mai zafi kan muhimman wurare a Iran.

Iran ta kara ɓarin wuta a Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa Iran ta harba makamai masu linzami zuwa wasu sassan Isra’ila da sanyin safiyar ranar Asabar, 21 ga Yuni.

Daga cikin yankunan da Iran ta yi wa ɓarin wuta a Isra'ila a wannan rana har da unguwar Holon, inda aka hangi gobara da hayaki na tashi.

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa wannan rikicin na iya ɗaukar lokaci mai tsawo, la'akari da yadda ƙasashen biyu ke kallon juna a matsayin abokan gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »