Yaƙin Iran da Isra'ila Ya Yi Gagarumar Ɓarna, An Kashe Mutane Sama da 600

Yaƙin Iran da Isra'ila Ya Yi Gagarumar Ɓarna, An Kashe Mutane Sama da 600

  • Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan adam (HRANA) ta bayyana cewa Isra'ila ta kashe sama da mutum 650 a hare-haren da ta kai Iran a mako guda
  • Rahoton ƙungiyar ya nuna cewa daga cikin waɗanda suka mutu akwai fararen hula da sojoji da kuma wasu da ba a iya tantance su ba
  • Rikici ya ɓarke tsakanin ƙasashen biyu tun bayan da Isra'ila ta kai hari wuraren aikin nukiliyar Iran, inda ta ce ta yi haka don kare kanta daga barazana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Sama da mutane 650 sun mutu a kasar Iran sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke ci gaba da kai wa tsawon mako guda.

Wata kungiyar kare hakkin dan adam da ke Amurka, Human Rights Activists News Agency (HRANA), ce ta bayyana hakan a rahoton da ta tattara kan rikicin Iran da Isra'ila.

Isra'ila ta kashe ɗaruruwan mutane a Iran.
Rahoton wata kunguya ya nuna adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Iran Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An kashe mutane sama da 600 a kasar Iran

Ƙungiyar ta ce fiye da mutane 650 sun mutu a Iran sakamakon ruwan bama-bamai da Isra’ila ke yi a ƙasar a mako guda da ya wuce, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

A cewar rahoton da HRANA ta fitar a ranar Juma’a, mutane 657 ne aka tabbatar sun mutu, sannan wasu 2,037 sun jikkata a harin sama da aka kai a sassa daban-daban na kasar Iran.

Gwamnatin Iran dai ba ta fitar da adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata a wannan rikici ba har kawo yanzu.

Yadda aka gano waɗanda suka mutu a Iran

HRANA ta ce tana samun bayanai ne daga wani wasu masu ba ta rahoto daga cikin kasar Iran, da kuma bayanan da ke fitowa fili.

Kungiyar ta bayyana cewa cikin wadanda suka mutu, akwai akalla fararen hula 263 da kuma sojoji 164, yayin da wasu 230 da suka rasu ba a tantance su ba tukuna.

Har ila yau, HRANA ta ruwaito cewa an yi wa ababen more rayuwa na Iraniyawa mummunar barna, ciki har da wani makami da faɗa kan asibitin yara a Tehran, duk da ba a samu rahoton rauni ko mutuwa a nan ba.

Shugaban Iran da Firaministan Isra'ila.
An fara fitar da alkaluman rayukan da aka rasa a yakin Iran da Isra'ila Hoto: @Netanyahu, Getty Images
Asali: Getty Images

Isra'ila ta lalata muhimman abubuwa a Iran

A yankin Ilam da ke yammacin Iran, wata tashar kashe gobara ta lalace, sannan harin da Isra’ila ta kai wata masana’antar kera mota a yammacin Iran ya haddasa gobara mai girma.

Duk da haka, Isra’ila ta dage cewa burinta shi ne ta hana Iran mallakar makaman nukiliya, wanda take kallon hakan a matsayin barazana ga rayuwarta ta kasa da kasa, rahoton AP News.

Zanga-zanga ta ɓarke a birnin Tehran

A wani labarin, kun ji cewa mazauna Iran sun fito zanga-zanga a Tehran da wasu birane domin nuna goyon bayansu ga jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Hakanan jama'a sun gudanar da zanga-zangar a biranen Tabriz a Arewa maso Yammacin Iran da Shiraz a Kudancin kasar.

Wannan dai na zuwa ne mako ɗaya bayan yaƙi ya ɓarke tsakanin Iran da Isra'ila, wanda jamhuriyar musuluncin ta zage damtse wajen maida martani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »