Iran Ta Jefa Yahudawa Sama da 8,000 cikin Mawuyacin Hali da Ta Kai Hare Hare kan Isra'ila
- Yahudawan Isra'ila aƙalla 8,000 sun rasa gidajensu da ƙasar Iran ta ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya tun makon jiya
- Rahoton asusun diyya da harajin dukiyoyi na Isra'ila ya nuna cewa mutane sama da 30,000 suka shigar da buƙatun neman diyyar gine-ginesu da aka rusa
- A yau Juma'a, 20 ga watan Yuni, 2025 aka shiga rana ta bakwai tun bayan fara musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Rahotanni sun bayyana cewa sama da Isra’ilawa 8,000 sun rasa matsuguninsu sakamakon hare-haren ramuwar gayya da Iran ke ci gaba da kai wa a ƙasar.
Wannan na zuwa ne a lokacin da rikicin da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran ke ƙara ta’azzara da kuma janyo ɗumbin hasara ga fararen hula.

Asali: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa dubban yahudawa da ake wa laƙabi da ƴan kama wuri zauna sun rasa gidajensu a ƙasar Isra'ila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Isra'ilawa akalla 8,000 sun rasa gidajensu
Idan za ku iya tunawa, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa yahudawa sun gudu, sun koma ƴan gudun hijira a tashoshin jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa.
Bayanai daga Asusun Diyya na Haraji kan Dukiyoyi na Isra'ila ya nuna cewa akalla buƙatu 30,000 aka karɓa daga jama’a masu neman a biya su diyyar lalacewar gidaje da motocinsu.
Waɗanda suka shigar da buƙatun neman diyya ga asusun na gwamnatin Isra'ila sun rasa gidajensu ne sakamakon hare-haren da Iran ta kai na ramuwa a ƙasarsu.
Wannan adadi mai yawa na yahudawan Isra'ila da suka rasa matsuguninsu yana nuna irin mummunar illar da rikicin ke da shi a cikin gida.
Wane mataki gwamnatin Isra'ila ta ɗauka?
A halin da ake ciki, hukumomi a Isra’ila suna ci gaba da tantance irin barnar da aka yi da kuma hanyoyin da za a bi wajen dawo da rayuwar waɗanda lamarin ya shafa.
Rahotanni sun nuna cewa ana fuskantar ƙalubale wajen samar sansanonin gudun hijira da za a sauke dubban mutanen da suka bar gidajensu saboda haɗarin tsaro da rushewar gine-gine.

Asali: Getty Images
Rikicin tsakanin Isra’ila da Iran ya ɗauki wani sabon salo tun bayan wani farmakin da aka danganta da Isra’ila a kan wani gini na diflomasiyya na Iran a Damascus.
Wannan farmaki dai shi ne musabbabin ramuwar gayyar da Iran ke yi, wanda a yanzu ya zama sanadin maida Isra'ilawa ƴan gudun hijira a wurare daban-daban.
Iran ta zafafa hare-hare kan Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa ƙasar Iran ta kai farmaki da makamai masu linzami kan muhimman wurare a birnin Beersheba da ke Kudancin Isra'ila.
Makamin ya taɓa cibiyoyi masu muhimmanci irin su ofishin Microsoft, cibiyar bincike da fasaha ta Gav-Yam Negev da kuma sansanonin sojin Isra’ila.
Iran ta lalata wani ɓangare na tashar jirgin ƙasa ta tsakiyar birnin Beersheba na ƙasar Isra'ila wanda ya jawo rufe wurin gaba ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng