An Bayyana Ƙasa 1 da Za Ta Iya Kare Iran yayin da Amurka Ke Shirin Kai Hari Tehran

An Bayyana Ƙasa 1 da Za Ta Iya Kare Iran yayin da Amurka Ke Shirin Kai Hari Tehran

  • Iran ta dade tana tallafa wa kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a Gabas ta Tsakiya domin samun kariya daga tasirin Isra’ila da Amurka
  • Bayan Isra’ila ta kai hari cikin kasar Iran, kawayenta kamar Hezbollah da Houthi sun yi shiru, ba su ma ce uffan ba a matsayin martani
  • Sai Rasha ce kaɗai ta fito ta nuna goyon baya, tana gargaɗin cewa shisshigin Amurka zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rikici mai muni

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Iran - Kasar Iran ta shafe shekaru tana tallafa wa kungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da gwamnatocin siyasa a Gabas ta Tsakiya.

Iran tana yin haka ne domin kafa “AoR”, watau abin da ta kira da wata kungiyar 'yan fito-na-fito da kasashen Isra’ila da Amurka.

Yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare Tehran, kawayen Iran sun ki shiga wannan fada
Babban jagoran kasar Iran, Ali Khamenei tare da shugaban kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Amma bayan Isra’ila ta kai jerin hare-hare a cikin Iran a ƙarshen mako da ya gabata, wadannan kawayen na Iran sun yi gum da bakunansu, ba wanda ya ce ko uffan, inji rahoton ABC News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ko da yake Amurka, babbar kawar Isra’ila, ta bayyana yadda za ta iya shiga faɗan, yanzu ƙungiya ɗaya daga cikin masu biyayya ga Iran ta fito fili ta kare ta.

Yadda Iran ke samar da kawaye a Gabas ta Tsakiya

Tun daga shekarun 1970, Iran ta gina wata ƙungiya ta abokanta a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da Hezbollah a Lebanon, Houthi a Yemen, wasu ƙungiyoyi a Iraq.

Ana zargin Iran ta karfafa Hamas a Gaza da West Bank, duk da nufin su ɗauki fansa idan aka kai hari kan Iran ko mabiyanta.

Amma masana tsaro kamar Dr. Andreas Krieg daga kwalejin King’s da ke London sun bayyana cewa irin wannan haɗin gwiwar ba zai iya amfanar Iran ba a yanzu.

A rahoton da kwalejin ta wallafa a shafinta na intanet, Dr. Andreas Krieg ya ce:

“Yanzu ba kamar da ba ne, domin kowa yana fama da kansa ne a halin da ake ciki."

A cewar Ian Parmeter, tsohon jakadan Ostareliya a Lebanon, Iran na cikin mafi raunin hali da ta shiga cikin shekaru 40 da suka wuce.

Ian Parmeter ya ce:

“Babu wata daga cikin kawayenta da za ta iya kawo mata dauki a yanzu, komai ya canja, ba kamar da ba.”

Ya ƙara da cewa yakin da Hamas ta shafe shekaru biyu tana yi da Isra’ila ya rage ƙarfinta matuƙa, yayin da gwamnati Bashar al-Assad a Syria ta karye bayan Hezbollah ta gwabza fada da Isra'ila na wata biyu.

China, Rasha da Koriya za su shiga rikicin?

Iran na cikin wata kungiyar kawance ta duniya mai lakabin “CRINK” wadda ke nufin China, Russia, Iran da Korea ta Arewa, a cewar wani rahoton Iran Daily.

China ta la’anci hare-haren Isra’ila kan Iran, amma ta tsaya ne da kiran a zauna a teburin sulhu don kawo karshen rikicin.

Koriya ta Arewa ma ta bayyana harin da Isra’ila ta kai a matsayin “laifi a yaƙi” amma ba ta nuna wani taimako kai tsaye ga Iran ba.

Shugaban kasar Rasha ya ce idan Amurka ta shiga fadan Iran da Isra'ila, to rikici mai muni zai barke a Gabas ta Tsakiya
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kasa 1 da za ta iya shigarwa Iran fada

Rasha ce kadai ta fito fili ta goyi bayan Iran, inda Shugaba Vladimir Putin ya nuna rashin amincewa da harin kuma ya yi gargaɗi cewa duk wani shisshigi daga Amurka zai iya haddasa rikici mai muni da za a kasa iya dakatarwa.

Shugaba Putin ya shaida wa duniya cewa:

"Rasha tana da kusanci sosai da Iran a halin yanzu, kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da jiragen yaki marasa matuki da muke amfani da su a yaki da Ukraine.
"Saboda haka, Rasha na da wani bashi a wajen Iran saboda wadannan jiragen, amma a lokaci guda, akwai kyakkyawar alaka ta kashin kai tsakanin Putin da Netanyahu."

Iran ta ragargaza cibiyar kimiyyar Isra'ila

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Isra’ila ta jima tana kai hare-hare kan masana nukiliyar Iran, sai dai yanzu masana kimiyyar ta sun fara shiga cikin hatsarin mayar da martani.

Iran ta harba wani makami mai linzami kan cibiyar bincike ta Weizmann a Isra’ila, inda ya lalata dakunan bincike da kayan aiki masu mahimmanci.

Ko da yake ba a rasa rai ba, harin ya razana Isra’ila, yayin da Iran ke cewa hakan martani ne kan kisan da aka yi wa masananta a baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »