An Gano Makamin Nukiliyan Iran da Ya Gagari Isra'ila, Kasa 1 ce Za Ta Iya Tarwatsa Shi

An Gano Makamin Nukiliyan Iran da Ya Gagari Isra'ila, Kasa 1 ce Za Ta Iya Tarwatsa Shi

  • Wani katafaren makamin nukiliya da ke karkashin dutse a Fordo, kusa da birnin Tehran, yana barazana ga Isra’ila
  • Masana sun ce bama-baman Isra’ila ba za su iya shiga zurfin da Fordo ke ciki ba sai dai na Amurka ne kadai zai iya hakan
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Iran da Isra'ila kusan mako guda kenan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - A cikin wani kogi a Kudu da birnin Tehran na kasar Iran ne aka boye wani katafaren makamin nukiliya.

Majiyoyi sun ce an boye makamin da ke da matukar muhimmanci ga burin Iran na nukiliya.

Makamin nukiliyan Iran da ya gagari Isra'ila
Akwai makamin da ke karkashin kasa da ya fi karfin Israel. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Makamin Iran da ya gagari Isra'ila

Rahoton BBC News ya ce a kullum kasar Isra'ila na kokarin tarwatsa su dalilin yaƙi da ake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ko da yake Isra’ila ta mamaye sararin samaniyar Iran, amma har yanzu cibiyar Fordo da ke karkashin kasa ta gagare ta.

An ce makamin na karkashin kasa da ta bi hanyar jirgin kasa tsakanin Birtaniya da Faransa.

Amurka ce kadai ake ganin tana da bam da zai iya tarwatsa Fordo, wanda hakan na iya kara tsananta yaki a Gabas ta Tsakiya.

An gina Fordo ta ne a karkashin tsaunuka masu wahalar shiga a Arewacin kasar Iran da ke yankin Asia.

An tsara ginin ne domin ya iya jure hare-haren sama, inda karkashinsa ba zai iya fuskantar bama-bamai na yau da kullum ba.

Katafaren makamin nukiliyan Iran da aka boye a karkashin kasa
An gano makamin Iran da Amurka ne kawai ke da karfin tarwatsa shi. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Yadda aka tsare makamin nukiliyan Iran

Cibiyar Fordo asali wasu ramuka ne da sojojin juyin juya halin Iran ke amfani da su, sai Iran ta amince da wanzuwarsu a 2009 bayan bayanan leken asirin kasashen Yamma.

An yi imanin cewa wurin yana da manyan ramuka biyu da ke dauke da injinan sarrafa sinadarin uranium, da kuma wata hanyar sadarwa da ramuka kanana.

Wurin yana da shinge mai zagaye da shi da kuma wurin binciken masu shiga da fita guda daya.

Ana tunanin akwai hanyoyi shida da ke kaiwa zuwa cibiyar da ke karkashin kasa, cewar rahoton CBS News.

Fordo ya zama kalubale musamman ga rundunar sojan sama ta Isra’ila saboda zurfin da aka gina cibiyar a karkashin kasa.

Domin tarwatsa wurin, sai da makamin da zai iya shiga cikin karkashin kasa mai zurfi sosai kafin ya tashi.

Isra’ila na da makamai masu karfi, amma ba su wuce zurfin 10m (33ft) ba, Amurka ce kadai ke da wani bam: GBU-57 MOP mai nauyin 13,000kg.

Iran/Isra'ila: Majalisar Dinkin Duniya ta magantu

Mun ba ku labarin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a gaggauta kawo karshen rikicin Iran da Isra’ila ta hanyar tattaunawar diflomasiyya.

Majalisar ta ce ya zama dole a kare fararen hula yayin da hare-haren makamai ke cigaba da halaka mutane a birane daban-daban.

Jakadan Iran ya ce hare-haren Isra’ila kan gine-ginen nukiliya barazana ne ga lafiyar jama'a, yana kira da a hukunta kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »