Isra'ila Ta Kai Mummunan Hari Tehran, Ta Ragargaza Gidan Talabijin Kasar Iran
- Isra'ila ta kai sabon farmaki gidan talabijin mallakin gwamnatin Iran a Tehran, yayin da mai gabatar da shiri take jawabi kai tsaye
- Kafin harin, ministan tsaron Isra'ila ya ce "gidan farfaganda na Iran na dab da bacewa," yana mai gargadar mazauna arewacin Tehran
- Sai dai gwamnatin Iran ta yi Allah wadai da harin, wanda ta kira "laifi a yaki," inda ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki mataki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Iran - An tabbatar da cewa Isra'ila ta samu nasarar farmakar gidan talabijin mallakin kasar Iran a ranar Litinin kamar yadda ministanta ya yi alkawari.
An rahoto cewa Isra'ila ta ragargaza gidan talabijin din Iran a dai dai lokacin da wata mai gabatar da shirye-shirye take magana a shirin kai tsaye.

Asali: Getty Images
Bidiyon da wakiliyar BBC, Nafiseh Kohnavard, ta wallafa a shafinta na X, ya nuna lokacin da aka katse shirye-shiryen kai tsaye da gidajen talabijin din ke gabatarwa sakamakon fashewar wani abu da ya cika ɗakin da ƙura.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
"Za mu kawar da talabijin da rediyon Iran" - Isra'ila
A ranar Litinin, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana racewa “gidan farfaganda da tayar da zaune tsaye na Iran na dab da bacewa”, bayan gargaɗin da aka yi wa mazauna Tehran da ke kusa da gidan talabijin.
A cikin wata sanarwa da ya ya fitar, kamar yadda rahoton France24 ya nuna, Israel Katz ya ce duk kafofin farfaganda na Iran za su shude.
Rahoton ya ce sojojin Isra’ila sun bukaci mazauna unguwar District 3 a arewacin Tehran su bar yankin saboda za su kai hare-hare.
Wannan yanki na daga cikin manyan wurare masu walwala, inda akwai asibitoci hudu, cibiyar da ke kula da ‘yan sanda, da kuma gidan talabijin din IRIB.
Iran ta yi martani da Isra'ila ta farmaki gidan talabijin
Gwamnatin Iran ta soki harin da Isra’ila ta kai kan ginin talabijin dinta a Tehran, inda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya bayyana shi a matsayin “mummunan aiki” da kuma “babban laifi a yaki”.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Esmaeil Baqaei ya ce:
"Duniya dai tana kallo: Farmakar ofishin kafar watsa labaran Iran (IRIB) ana tsakiyar watsa shirye-shirye kai tsaye mummunan laifi a yaki ne.
"Gwamnatin Isra'ila ce mafi muni a adawa da fadin gaskiya, kuma ita ce a sahun farko wajen kashe 'yan jarida da ma'aikatan watsa labarai.
“Ya zama dole Majalisar Dinkin Duniya ta dauki mataki yanzu don hana wannan dan ta’adda mai kashe jama’a ci gaba da aikata munanan laifuffuka a kan mutanenmu."

Asali: Getty Images
“Ban san yawan abokan aikin da ke ciki ba” – Dan Jarida
Sai dai, an rahoto cewa ya zuwa yanzu, gidan talabijin na kasar Iran ya ci gaba da watsa shirye-shiryensa bayan wannan harin da aka kai masa.
“Ina bene na farko lokacin harin, ban san yawan abokan aikina da ke ciki ba – ko wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata."
- In ji Younes Shadlou, dan jaridar IRIB, a wata hirar bidiyo da kamfanin ISNA na Iran ya watsa a shafinsa na X.
Younes Shadlou ya kara da cewa:
“Duk da barazanar, mun ci gaba da watsa shirye-shirye don nuna karfin Iran. Isra’ila ta yi tunanin za ta karya mu ta hanyar kai hari kan IRIB. Za ta yi babbar nadama yanzu."
Kalli bidiyon lokacin da aka farmaki gidan talabijin din a nan kasa:
Sabon harin Iran ya hallaka mutane 8 a Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Iran ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra'ila, inda aka ce mutane takwas sun mutu a birnin Tel Aviv a ranar Litinin, 16 ga Yuni.
Sai dai a hannu guda, Isra'ila ta gargadi mazauna Tehran da suka haura mutane 330,000 da su gaggauta barin garin kafin ta kai farmaki.
Isra'ila ta kuma shaida cewa ta sami cikakken rinjaye a sararin samaniyar Iran, inda ta ce ta lalata wuraren harba makamai 120 na kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng