Asiri Ya Tonu: Iran ta Kama Mai Yi wa Isra'ila Leken Asiri, An Kashe Shi

Asiri Ya Tonu: Iran ta Kama Mai Yi wa Isra'ila Leken Asiri, An Kashe Shi

  • Hukumomin Iran sun tabbatar da kisa ta hanyar rataya ga wani mutum mai suna Esmail Fekri da aka samu da laifin leƙen asiri ga hukumar Mossad ta Isra’ila
  • An kama Fekri tun a watan Disamba na 2023 bayan wani gagarumin bincike da jami’an tsaro na Iran suka gudanar
  • Kotun kolin kasar ta tabbatar da hukuncin kisa bayan shaidun da suka haɗa da bayanan kwamfuta, kudi daga Mossad da amsa laifi daga Fekri da kansa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Wani rahoto daga kafafen yada labaran Iran ya tabbatar da cewa gwamnatin kasar ta aiwatar da hukuncin kisa ga wani mutum da aka samu da laifin leƙen asiri ga Isra’ila.

An bayyana sunan mutumin mai suna Esmail Fekri yana hada kai da hukumar leken asirin Isra'ila ta Mossad.

An kama mai leken asiri a Iran
Iran ta kashe mai yi wa Isra'ila leken asiri. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Rahoton Tehran Times ya nuna cewa an kashe mutumin a safiyar Litinin, bayan kotu ta same shi da laifin alaka da Mossad da kuma miƙa musu bayanan tsaro masu matuƙar muhimmanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Hukumar ISNA ta ce Fekri ya faɗi gaskiyar cewa yana hulɗa da jami’an leƙen asirin Isra’ila guda biyu, kuma yana miƙa musu bayanai ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa a boye.

Yadda aka kama Fekri da laifin leƙen asiri

Bincike daga bangaren shari’a ya nuna cewa Esmail Fekri ya fara hulɗa da jami’an Mossad tun kafin a kama shi a watan Disamba na bara.

Rahoton BBC Hausa ya bayyana cewa ya rika tattara bayanai dangane da wuraren soja, bayanan wasu manyan jami’an tsaro da kuma bayanan sirri na harkokin cikin gida.

An gano cewa yana mika bayanai ne ta hanyar na’urorin sadarwa masu matuƙar tsaro da aka umarce shi da ya kafa.

Hakanan jami’an Mossad sun ba shi umarnin kafa asusun ajiyar kuɗi na yanar gizo domin karɓar kuɗin aiki daga Isra’ila.

Bayanin kotu kan dan leken asiri a Iran

Bayan an kama shi, jami’an tsaro sun yi bincike kan wayoyinsa da kwamfutarsa, inda suka gano saƙonnin sirri da umarnin da jami’an Mossad suka ba shi.

A lokacin shari’a da aka gudanar a gaban lauyansa, kotu ta tabbatar da samun sa da laifi bisa shaidun da suka haɗa da takardu, saƙonni, bayanan kwamfuta, da kuma kudin da ya karɓa.

Kotu ta yi masa hukunci ne bisa laifin karya dokar da aka kafa domin kare zaman lafiya da tsaron ƙasa.

An rataye dan leken asirin Isra'ila a Iran

Bayan da kotun koli ta duba hukuncin farko, ta tabbatar da shi, sannan aka aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda doka ta tanada.

Wannan mataki na Iran na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin tsakanin Iran da Isra’ila ke kara kamari.

Kotu ta kama dan Iran da laifin leken asiri
Kotu ta kama dan Iran da laifin leken asiri. Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Sai dai kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasar Iran ta yi Allah wadai da hukuncin tana cewa ba a masa adalci ba.

A sakon da ta wallafa a shafinta na X, kungiyar ta ce matakin zai zamo barazana ga sauran 'yan kasar Iran.

Pakistan za ta taya Iran fada da Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin kasar Iran ta tabbatar da cewa ta samu tabbacin goyon bayan Pakistan.

Iran ta bayyana cewa Pakistan ta yi alkawarin kai hari da makamin nukiliya zuwa Isra'ila idan ta kai harin da nukiliya Iran.

Ministan tsaron Pakistan ya ce sun tanadi makamin nukiliya ne domin kare kansu daga makiya ba domin zalunci ba kamar Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »