Hankula Sun Tashi, An Samu Barazanar Dasa Bam a Jirgin Kamfanin Air India bayan Ya Tashi
- Wani jirgin saman Air India ya yi saukar gaggawa a birnin Phuket na ƙasar Thailad jim kaɗan bayan tashinsa ranar Juma'a
- Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya dawo filin da ya tashi ne bayan samun sakon barazana da ke nuna an dasa bam a ɗakin wanka
- Kawo yanzu dai ba a ga wani bam ba a jirgin bayan sauke duka fasinjoji cikin tsaro ba tare da komai ya same su ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Phuket, Thailand - Wani jirgin fasinja na kamfanin Air India da ya tashi daga Phuket zuwa New Delhi, babban birnin Indiya ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama a Phuket.
An ruwaito cewa jirgin sama ya yi gaggawar komawa filin jirgin ne bayan da aka samu sakon barazanar dasa bam a cikin ɗakin wanka na jirgin bayan ya tashi.

Asali: Twitter
Jaridar Reauters ta ce jirgin mai lamba AI 379, wanda ke ɗauke da fasinjoji 156, ya koma filin jirgin saman Phuket lafiya kuma an sauke duka fasinjoji cikin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Wane hali fasinjojin jirgin saman ke ciki?
Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta ƙasar Thailand ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jirgin ya dawo lafiya kuma duka waɗanda ke cikinsa na cikin tsaro.
An tattabar da cewa ba a samu wani bam a ciki ba da aka bincike jirgin gaba ɗaya bayan ya yi saukar gaggawa.
Shugaban filin jirgin saman Phuket, Monchai Tanode, ya bayyana a taron manema labarai cewa an samu saƙon barazana da ke nuna an dasa bam a ɗakin wanka na jirgin bayan ya tashi.
Ƴan sanda sun fara bincike kan lamarin
"’Yan sanda sun kama wasu da ake zargi domin tambayoyi, amma ba su iya tabbatar da wanda ya rubuta saƙon ba,” in ji shi.
Wani jami’in Air India, Debasish Choudhury, ya ce an fara zargin mutane uku, amma daga bisani duk an wanke su daga zargi, rahoton The Phuket News.
Wannan lamari na zuwa ne kwana guda bayan wani jirgin Air India ya yi hatsari a Ahmedabad, inda sama da mutane 240 suka mutu.
Rahotanni sun nuna cewa a cikin watanni 10 na farko na 2024, an samu fiye da kira da saƙonni 1,000 na ƙarya da ke barazanar dasa bama-bamai a manyan filayen jirgin sama da jiragen Indiya, ninki goma na wanda aka samu a 2023.
Hukumomi sun bukaci jama'a da su kasance masu fahimta da haɗin kai yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Jirgin ɗauke da mutane 62 ya rikito ƙasa a Brazil
A wani rahoton, kun ji cewa wani jirgin sama da ya ɗauko fasinjoji 62 ya yi haɗari ranar Jumu'a, a kusa da birnin Sao Paulo na kasar Brazil.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya taso ne daga filin sauka da tashin jiragen sama na Cascavel da nufin zuwa Sao Paulo amma ya gamu da hatsari.
Kamfanin sufurin jiragen sama na VoePass, masu jirgin da ya yi hatsarin sun bayyana cewa ya ɗauko mutane 58 da ma'aikata huɗu.
Asali: Legit.ng