Yadda Mahajjata Suka Take Gargaɗin Minista game da Hawa Dutsen Arafah a Saudiyya

Yadda Mahajjata Suka Take Gargaɗin Minista game da Hawa Dutsen Arafah a Saudiyya

  • Mahajjata sun tsallake gargaɗin zafin rana da hukumomin Saudiyya suka yi, sun hau dutsen Arafah yau Alhamis, 9 ga watan Dhul Hijjah
  • Rahotanni sun bayyana cewa dubban mahajjata ne suka mamaye dutsen domin gudanar da ibadu da addu'o'i yayin aikin hajjin 2025
  • Tun farko dai hukumomin Saudiyya sun shawarci mahajjata su yi zamansu a tantuna daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma saboda zafin rana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Dubban musulmi da suka je aikin hajjin bana 2025 ciki har da Najeriya sun taru a dutsen Arafah a yau Alhamis, 9 ga watan Dhul Hijjah, 1446.

Mahajjatan sun fita sun hau dutsen Arafah duk da gargaɗin zafin rana mai tsanani, domin yin addu'o'i da neman yardar Allah a wannan rana mai tarin albarka.

Alhazai sun yi hawan Arafah.
Musulmi sun hau dutsen Arafah duk da gargaɗin zafin rana a Saudiyya Hoto: Inside The Haramain
Asali: Facebook

Ministan Hajjin Saudiyya ya gargaɗi mahajjata

Vangaurd ta ce Ministan Hajj na Saudiyya ya bayar da gargaɗi a yau cewa mahajjata su zauna cikin tantuna daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma saboda hadarin kamuwa da zazzaɓin rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Tsayuwar Arafah na ɗaya daga cikin rukunan aikin Hajji, inda rahotanni suka tabbatar da cewa mahajjata sun mamaye dutsen duk da zafin ranar da ake yi.

A ranar Lahadi, Cibiyar Kula da Yanayi ta Saudiyya (NCM) ta yi hasashen za a yi rana mai tsananin zafi a lokacin Hajjin 2025.

NCM ta bukaci mahajjata da su yi taka-tsantsan yayin da matakin zafi zai iya kaiwa tsakanin 40°C zuwa 47°C da rana.

Mahajjata sun mamaye dutsen Arafah

Sai dai, mahajjata mata da maza sun ci gaba da tafiya daga nesa, suna hawan Dutsen Arafah don yin addu’a da neman gafara.

Yusuf Hassan, ɗaya daga cikin mahajjatan Najeriya, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa:

“Na san da gargaɗin, amma ba zan iya jurewa ba, domin na yi wa kaina alƙawari cewa zan hau Dutsen Arafat idan Allah ya ba ni damar zuwa Hajj. Alƙawari ne da na cika.”

An ruwaito cewa yawancin mahajjata sun kiyaye shawarar gwamnati, inda suka tsaya cikin tantuna suna karatun Alƙur’ani da addu’o’i cikin natsuwa.

Yadda jirage ke shawagi a saman dutsen

A sama, an ga jiragen sama masu saukar ungulu na shawagi, yayin da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ke zagaye ko’ina suna jagorantar mahajjata yadda za su bi dokokin ƙasashensu da na hajji.

Hazaifa Sani, wani mahajjaci daga Najeriya ya ce:

“Ziyartar Dutsen Arafah wani babban abu ne da kowanne Musulmi bai kamata ya rasa ba. Wannan rana ita ce mafi alkhairi ga Musulmi a kowace shekara, kuma jin daɗin da kake ji a nan ba a iya kwatanta shi.”
Hawan Dusten Arafah a lokacin hajji.
Wasu mahajjata sun bayyana cewa ba za su iya haƙurada hawa dutsen Arafah ba Hoto: Inside The Haramain
Asali: Facebook

An kuma ga mahajjata da dama a wajen tantuna, sun daga hannuwa sama cikin tsananin ibada, hawaye na zuba a fuskokinsu, suna rokon Allah buƙatunsu.

Dutsen Arafah na da matuƙar muhimmanci a addinin Musulunci, domin a nan ne Annabi Muhammad (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta bankwana.

Mahajjaci daga Kano ya rasu Makkah

A wani labarin, kun ji cewa wani mahajjaci daga jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, ya rasu a birnin Makkah da ke ƙasar Saudiyya.

Mai magana da yawun hukumar kula da jin daɗin alhazan Jihar Kano, Malam Suleiman Dederi, ne ya tabbatar da rasuwar Shu'aibu.

Ya shaidawa manema labarai a birnin Makkah cewa kafin su baro Kano, Shu'aibu yana fama da cutar gyambo da hawan jini sama sama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »