Trump Ya Hana Wasu Kasashen Musulmai da Sauransu Shiga Amurka
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya hannu kan dokar hana mutane daga ƙasashe 12 shiga ƙasar, ciki har da Iran
- Donald Trump ya bayyana cewa matakin zai kare Amurkawa daga “mutane masu haɗari” da ke fitowa daga kasashe ƙetare
- Haramcin zai fara aiki daga ranar 9 ga Yuni, 2025, kuma yana ɗaya daga cikin alkawuran yaƙin neman zaɓensa na 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka da ta haramta wa ‘yan ƙasashe 12 shiga Amurka.
Donald J. Trump ya ce an dauki matakin ne domin kare lafiyar Amurkawa daga haɗarin da ke zuwa daga wasu kasashen waje.

Asali: Getty Images
Rahoton BBC ya ce matakin na iya jawo ƙalubale daga lauyoyi da kungiyoyi masu kare ‘yancin dan Adam, musamman ganin cewa Joe Biden ya taba rusa irin dokar bayan Trump ya kafa ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ƙasashen da abin ya shafa sun haɗa da Afghanistan, Iran, Haiti, Libya, Somalia, Sudan, Yemen, da wasu ƙasashen Afirka da Asiya, kuma za a fara aiwatar da dokar ne daga ranar 9 ga Yuni, 2025.
Kasashen da Trump ya hana shiga Amurka
Rahoton Reuters ya nuna cewa Donald Trump ya sanar da haramcin ne a wani bidiyo inda ya ce ba za su lamunci mutanen da ke da niyyar cutar da ƙasar su ba.
Rahotanni sun nuna cewa Donald Trump ya kara da cewa ana iya ƙara wasu ƙasashe a jerin a nan gaba.
Ƙasashen da aka haramta su gaba ɗaya su ne Afghanistan, Myanmar, Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan da Yemen.
Wasu za su samu rangwame kan dokar Trump
A cewar sanarwar da ofishin Trump ya fitar, akwai wasu rukunin mutane da haramcin ba zai shafe su ba.
Wadanda za a yi wa afuwa akwai ‘yan wasa da ke zuwa manyan gasar wasanni, ‘yan Afghanistan da ke da takardun izinin shiga kasar da kuma masu shaidar wata ƙasa daban da ba a haramta ba.
A cewar umarnin, wadanda aka riga aka ba biza kafin 9 ga Yuni ba za su rasa izinin shiga Amurka ba, amma sababbin masu neman izini daga waɗancan ƙasashen za a hana su.
Yadda Biden ya soke dokar Trump a baya
Tun lokacin da ya ke shugaban kasa a wa'adi na farko, Trump ya sanya irin wannan doka a 2017, wacce ta shafi ƙasashe Musulmi guda bakwai, ciki har da Syria da Iraq.

Asali: Getty Images
Sai dai tsohon shugaban kasa Joe Biden, wanda ya gaje shi a 2021, ya soke dokar, yana mai cewa ta tauye mutunci da darajar Amurka.
Donald Trump ya ziyarci kasashen Musulmi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ziyarci wasu kasashen Musulmi a Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kasar Saudiyya, Qatar da UAE na cikin manyan kasashen Larabawa da Trump ya je.
Legit ta rahoto cewa shugaba Donald Trump ya tattauna lamura da suka shafi kasuwanci da tsaro yayin da ya kai ziyarar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng