An Shiga Fargabar Juyin Mulki a Afrika, An Nemi Shugaban Kasar Côte d'Ivoire An Rasa

An Shiga Fargabar Juyin Mulki a Afrika, An Nemi Shugaban Kasar Côte d'Ivoire An Rasa

  • Rahotanni sun nuna cewa ana cikin rikici mai tsanani a birnin Abidjan, inda aka ji harbe-harbe, kuma mutane sama da 30 sun mutu
  • Lamarin ya kidima jama'a da tuni suka fara fargabar ko an yi juyin mulki bayan an daina jin duriyar shugaban kasa, Alasanne Ouattara
  • Rikice-rikicen da ake samu sun samu sun samo asali ne daga zargin da jama'a ke yiwa gwamnatin Côte d'Ivoire na biyewa Amurka da Faransa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Ivory Coast – Rahotanni daga kasar Côte d'Ivoire na nuni da cewa ana cikin tashin hankali da rudani saboda fargabar juyin mulki.

Mazauna kasar, musamman a Abidjan, sun bayyanacewa sun ji karar harbe-harbe a wasu sassan birnin yayin da ake tsoron an kifar da gwamnatin Alasanne Ouattara.

Alasanne
An fara fargabar juyin mulki a Ivory Coast Hoto: Alasanne Ouattara
Asali: Facebook

Jaridar Tanzania Times ta ruwaito cewa akalla mutane 33 ne suka mutu cikin awanni 48 da suka gabata, yayin da rikici ke ƙara tsananta a muhimman unguwannin babban birnin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ana rade-radin juyin mulki a Côte d'Ivoire

Jaridar Daily Trust ta ce wannan tarzoma na da alaƙa da fushin jama'a kan gwamnatin Shugaba Alassane Ouattara kan salon mulkinta.

Jama'a na zargin gwamnatin da take haƙƙin ɗan adam, ƙara talauci, da kuma yin zama yar amshin shatan kasashen waje, musamman da Faransa da Amurka.

Alasanne
An nemi shugaban Ivory Coast an rasa Hoto: Alasanne Ouattara
Asali: Facebook

Masu zanga-zanga na zargin gwamnatin Ouattara da zama yin sake ana kara samun yawaitar dakarun rundunar AFRICOM a yankin.

Juyin mulki: Gwamnatin Côte d'Ivoire ta yi shiru

Duk da wannan halin, ba a samu wata tabbatacciyar hujja daga gwamnati ba, kuma ta ki bayyana halin da shugaban kasa ke ciki.

Wasu majiyoyi na cewa ko dai Shugaba Ouattara ya ɓace, an kama shi ko kuma ya rasu, amma babu wata sanarwa daga hukumomin kasar da ta tabbatar da hakan.

A gefe guda kuma, masu fafutuka sun bayyana wasu daga cikin bidiyoyin da suka karade kafafen sada zumunta a matsayin masu cike da ruɗani kan zargin juyin mulki.

Kungiyoyin ƙasa da ƙasa da jakadun ƙasashe sun shiga shirin ko-ta-kwana saboda rashin tabbas da ke tattare da lamarin.

Rahoton na cewa kungiyoyin ƙasa da ƙasa da ofisoshin jakadanci sun bukaci jama'arsu da su zauna a gida tare da kiyaye dokokin tsaro.

Wannan ba shi ne karo na farko da Ivory Coast ke fuskantar rikici ba, domin ƙasar ta taɓa fuskantar juyin mulki a 1999, yakin basasa daga 2002 zuwa 2007 da kuma daga 2010 zuwa 2011, baya ga tawaye daga sojoji a 2017.

IBB ya karyata goyon bayan juyin mulki

A baya, mun wallafa cewa tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya karyata rahotan da ke danganta shi da goyon bayan dawo da mulkin soja a Najeriya.

Wata sanarwa da Mahmoud Abdullahi ya fitar a madadin ofishin watsa labarai na IBB ta bayyana cewa tsohon shugaban ba shi da wani shafi a kafar sada zumunta da aka yada zancen.

A baya wani shafin X mai suna @General_Ibbro ya wallafa wani saƙo da ke cewa IBB ya fi son mulkin soja fiye da na dimokuraɗiyya, lamarin da ya jawo cece kuce a tsakanin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »