Dangote da Abokinsa Sun Mallaki Katafaren Kamfanin Yawon Bude Ido a Kenya

Dangote da Abokinsa Sun Mallaki Katafaren Kamfanin Yawon Bude Ido a Kenya

  • Kamfanin Africa Travel Investments da ke da alaka da Aliko Dangote ya saye Pollman’s Tours and Safaris, babban kamfanin yawon buɗe ido a Kenya
  • Hukumar Kasuwanci ta Kenya (CAK) ta amince da cinikin ba tare da sharaɗi ba, inda aka tabbatar cewa ba zai shafi kasuwar yawon buɗe ido ba
  • An tabbatar da cewa babu wani ma’aikacin da zai rasa aiki yayin da Pollman’s ke shirin shiga sabon mataki na ci gaba da haɓaka harkokinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wani kamfani a harkar yawon buɗe ido da ke da alaka da Aliko Dangote ya kammala sayen Pollman’s Tours and Safaris — kamfanin yawon buɗe ido mafi tsufa a Kenya.

Hukumar Kula da Kasuwanci ta Kenya (CAK) ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar kwanan nan, inda ta ce ta amince da sayen cikin kashi 100 na hannun jarin kamfanin.

Pollman’s Tours and Safaris
Dangote da abokinsa sun mallaki kamfanin yawon bude ido a Kenya. Hoto: Dangote Industries|Pollman’s Tours and Safaris
Asali: Facebook

Rahoton Africa Business Insider ya nuna cewa CAK ta ce cinikin ba zai sauya tsarin kasuwar yawon buɗe ido a Kenya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ba za a rasa aiki a kamfanin su Dangote ba

Hukumar CAK ta bayyana cewa ta lura da irin tasirin da cinikin zai iya yi ga ayyukan yi da kananan ‘yan kasuwa.

Amma duk da haka, ta tabbatar da cewa ba za a samu rasa ayyuka ko durƙushewar ƙananan masana’antu ba.

Kamfanin Africa Travel Investments ya ce sayen kamfanin dama ce da ke da nufin kawo cigaba a fannin yawon buɗe ido.

Rahotan the Cable ya nuna cewa za a samu cigaba musamman wajen buɗe ƙofa ga sababbin masu yawon shakatawa daga sassa daban-daban na duniya.

Yadda su Dangote suka fara mallakar kamfanin

A Fabrairu kamfanin Alterra Capital da Dangote da attajiri Dave Rubenstein ke goyon baya ya zuba jari a kamfanin ARP Africa Travel Group da ke kula da Pollman’s Tours and Safaris.

Alterra Capital ya kuma saye kaso mai rinjaye na shahararren kamfanin shayi na Java Coffee a watan Janairu, wanda ke da rassa 73 a Kenya, Uganda da Rwanda.

Pollman’s Tours and Safaris da aka kafa tun shekaru da dama da suka wuce, ya ce sabon matakin zai ba shi damar shigowa da sababbin dabarun haɓaka harkokin yawon buɗe ido a Afirka.

Dangote
An ce ba za a rasa ayyuka a kamfanin da Dangote ya mallaka a Kenya ba. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Kamfanin ya ce zai ci gaba da girmama tarihi da tushe da ya gada, tare da kawo sababbin hanyoyi na shakatawa da ilimantar ga masu yawon buɗe ido kan kyawawan al’adun Afirka.

Ana sa ran Pollman’s zai zama ginshiƙi wajen ɗaukaka martabar Afirka a idon duniya ta hanyar yawon buɗe ido na zamani.

Dangote zai kafa kamfanin sukari a Ghana

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa zai kafa katafaren kamfanin sukari a kasar Ghana.

An bayyana cewa kamfanin zai taimakawa kasar Ghana wajen rage dogaro da shigo da sukari daga kasashen waje.

Dubban matasan nahiyar Afrika ne ake saka ran za su samu ayyukan yi daga kamfanin da zarar an kammala aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »