Tashin Hankali: An Harbe Fitacciyar Ƴar TikTok har Lahira Tana Tsaka da Yin Bidiyo

Tashin Hankali: An Harbe Fitacciyar Ƴar TikTok har Lahira Tana Tsaka da Yin Bidiyo

  • An harbe Valeria Marquez, fitacciyar ‘yar TikTok har lahira yayin da take yin bidiyo kai tsaye daga shagon yin kwalliya da gyaran gashinta
  • An ce wani mutumi ya zo wajen Valeria kafin ta iso shagon, inda daga baya ya dawo, kuma ya harbe ta yayin da take magana da masoyanta
  • Mutuwar Valeria ta biyo bayan kisan wata ‘yar takarar magajin gari a jihar Veracruz, lamarin da ke jaddada matsalar kisan gillar mata a Mexico

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Mexico - Valeria Marquez na yi wa mabiyanta na TikTok jawabi kai tsaye daga shagon gyaran gashinta a Zapopan, Mexico, lokacin da wani ya kawo mata saƙo

"Yar tsanar alade ce," inji Valeria, mai shekaru 23 da ta shahara a fannin kwalliya yayin da ta koma ga masu kallonta tana buɗe ɗan kwalin, tana murmushi.

An harbe 'yar TikTok har lahira tana tsakiyar yin bidiyo a Mexico
Shahararriyar 'yar TikTok, Valeria Marquez da aka kashe tana bidiyo. Hoto: @njuruh_ng
Asali: Twitter

An kashe 'yar TikTok tana tsakiyar yin bidiyo

Kwatsam sai aka ga matashiyar ta yanke jiki ta faɗi a kujerarta, jini na malala a kan teburin da ke gabanta, yayin da ake ci gaba da kallonta kai tsaye, inji rahoton CNN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

An rahoto cewa bidiyon da duniya ke kallo kai tsaye ya tsaye ne kawai lokacin da wani ya ɗauki wayarta, har ma masu kallo suka ɗan ga fuskarsa.

Ofishin babban lauyan jihar Jalisco, ya ce wani da ya shiga shagon gyaran gashinta ne ya harbe Valeria har lahira, yayin da suke binciken lamarin a matsayin kisan gilla.

Mutuwar Valeria, shahararriyar 'yar TikTok kuma mai mabiya sama da 100,000 a Instagram, ta girgiza ƙasar da ta daɗe tana fama da yawan kashe-kashen mata da ake yi.

Wanda ake zargin ya kashe 'yar TikTok din

A cewar mai magana da yawun ofishin lauyan jihar Jalisco, mutumin da ake zargin ya aikata laifin ya je shagon kafin Valeria ta iso, inda ya ce ita kadai yake so ta gyara masa gashi.

Mai magana da yawun ofishin ya ce mutumin ya sake komawa shagon gyaran gashin daga baya a wannan ranar, wanda shi ne lokacin da aka yi kisan, kamar yadda bidiyon ya nuna.

Ba a bayyana sunan wanda ake zargin ba, kuma a halin yanzu ba a binciken kisan a matsayin wanda ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu fataucin miyagun ƙwayoyi a yankin ba, inji rahoton Aljazeera.

An shiga har cikin shagon shahararriyar 'yar TikTok, an harbe ta har lahira a Mexico
Shahararriyar 'yar TikTok, Valeria Marquez da aka kashe tana bidiyo. Hoto: @njuruh_ng
Asali: Twitter

Ana yawan yi wa mata kisan gilla a Mexico

Kwanaki kaɗan kafin faruwar lamarin, an harbe wata mata, ƴar takarar kujerar magajin gari a jihar Veracruz har lahira yayin da take watsa shirye-shirye kai tsaye, tare da wasu mutane uku.

Duk da cewa ba duk kashe-kashen da suka shafi mata ake bincikawa a matsayin kisan gilla ba, amma ana ganin da yawa daga cikinsu kisan gillar ne.

A bara, an sami rahotannin kisan gilla 847 a faɗin ƙasar, da 162 a cikin watanni uku na farkon wannan shekara, a cewar alkaluman gwamnatin Mexico.

Dan TikTok ya mutu yana tsaka da yin bidiyo

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani shahararren ɗan TikTok da aka fi sani da Disturbing ya rasu yayin da yake daukar bidiyo kai tsaye a dandalin sada zumunta.

Ƴar jarida mai binciken kwakwaf, Temilola Sobola, ta tabbatar da mutuwar Disturbing, ta ce marigayin ya yanke jiki ya faɗi bayan fara watsa bidiyon.

Disturbing na faɗin kalamai masu zafi kan waɗanda ake zargi da hannu a mutuwar Mohbad ne kafin ya yanke jiki ya fadi a bidiyon da ya tada hankula.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »