Wanene Robert Prevost? Abin da Muka Sani game da Sabon Shugaban Kiristocin Duniya

Wanene Robert Prevost? Abin da Muka Sani game da Sabon Shugaban Kiristocin Duniya

  • Robert Francis Prevost shi ne sabon Fafaroma na 267, ya karɓi sunan Leo XIV, kuma shi ne Ba'amurke na farko a matsayin
  • A yayin da yake jawabi bayan nadinsa, Prevost ya yaba da ƙarfin imanin marigayi Fafaroma Francis da tasirinsa ga Rome
  • A cikin wannan rahoton, Legit Hausa, ta zakulo wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon shugaban Katolika na duniya
  • Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Amurka - An zabi Kadinal Robert Francis Prevost na kasar Amurka a matsayin shugaban Cocin Katolika na 267, domin jagorantar Kiristocin duniya.

Babban kadinal Dominique Mamberti ya sanar da zaben sabon Fafaroma ga taron jama'a da ke murna a harabar St Peter, yana mai faɗin shahararrun kalmomin Latin: "Habemus Papam", ma'ana "mun samu sabon Fafaroma".

Abubuwan da muka sani game da Prevost, sabon Fafaroma na duniya
Sabon zababben Fafaroma, Leo XIV, Robert Prevost, ya isa barandar Basilicar St Peter a karon farko, a ranar 8 ga Mayu, 2025. Hoto: Christopher Furlong
Asali: Getty Images

Da yake magana da Italiyanci, Robert Prevost mai shekaru 69 ya ce marigayi Fafaroma Francis ya kasance mutum mai ƙarfin imani, kuma abin alfaharin Romawa, inji Daily Trust.  

Ga wasu muhimman abubuwa biyar da muka sani game da sabon Fafaroma, Leo XVI:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

1. Haihuwa zuwa girma

An haifi Robert Prevost a Chicago a ranar 14 ga Satumba, 1955. Ya kasance ɗa ga Louis Marius Prevost da Mildred Martinez.

Mahaifinsa, wanda tsohon sojan ruwan Amurka ne a yakin duniya na biyu kuma shugaban makaranta, ya fito daga tsatson Faransa da Italiya, ita kuma mahaifiyarsa 'yar Spain ce.

Ya kammala karatun sakandare a ƙaramar makarantar St. Augustine a 1973, sannan ya sami digiri na farko a fannin lissafi a jami'ar Villanova a 1977.

Da ya yanke shawarar zama malamin majami'a, Prevost ya shiga makarantar Order of St. Augustine a watan Satumba 1977.

Ya yi rantsuwar farko ga ƙungiyar malaman majami'u a watan Satumba 1978 da kuma rantsuwar ƙarshe a watan Agusta 1981.

A shekarar da ta biyo bayan wannan, an ba Robert Prevost kwalin digiri na Master of Divinity daga kungiyar Catholic Theological da ke a Chicago.  

2. Yarukan da Robert Provest ya iya

Mujallar Forbes ta ce Prevost yana magana da Ingilishi, Spanish, Italiyanci, Faransanci, da Portuguese, kuma yana iya karanta Latin da Jamusanci.  

3. Shigar Prevost kungiyar malaman coci

An naɗa Prevost malamin cocin Archbishop Jean Jadot don Augustinians a garin Rome a ranar 19 ga Yuni, 1982.

An ce ya sami lasisi a fannin shari'ar Canon a 1984 da digiri na Doctor of Canon Law a 1987 daga kolejin PC, St. Thomas Aquinas a Rome.

Prevost ya shiga aikin wa'azi na Augustinian a garin Peru a 1985 kuma ya yi aiki a matsayin shugaban Territorial Prelature na Chulucanas daga 1985 zuwa 1986.

Ya koma garin Peru a 1988, inda ya shafe shekaru goma yana jagorantar makarantar malaman coci ta Augustinian da ke a Trujillo.

Ya kuma koyar da shari'ar Canon a makarantar malaman cocin diocesan kuma ya yi aiki a matsayin shugaban sashen koyar da shari'ar.

Prevost ya yi aiki a matsayin alkali a kotun majami'u ta yanki kuma mamba na Kwalejin Mashawarta na Trujillo. Sannan ya kuma jagoranci wata ikilisiya a wajen birnin.  

4. Prevost ya fuskanci suka a lokuta da dama

Prevost ya fuskanci suka daga masu fafutukar kare waɗanda malaman coci suka ci zarafin su dangane da yadda ya magance zargin cin zarafin jima'i a lokacin shugabanci ƙungiyar Augustinian da kuma a Peru.

Ƙungiyar masu fafutuka ta SNAP ta zargi Prevost da gazawa wajen ɗaukar mataki kan zargin cin zarafi da ya shafi Richard McGrath, tsohon shugaban makarantar Providence Catholic, inda ya bar shi a matsayinsa duk da zarge-zarge da aka dade ana yi.

Abubuwan sani game da Robert Prevost, sabon shugaban Kiristocin Duniya.
Sabon zababben Fafaroma, Leo XIV, Robert Prevost, ya isa barandar Basilicar St Peter a karon farko, a ranar 8 ga Mayu, 2025. Hoto:ALBERTO PIZZOLI / Contributor
Asali: Getty Images

5. Nadin Prevost a matsayin Fafaroma

An fara tunanin Prevost zai iya zama sabon shugaban cocin Katolika na duniya tun bayan bayan mutuwar Fafaroma Francis.

A shekarar 2023, Fafaroma Francis ya naɗa Prevost a matsayin shugaban Dicastery na Bishops, wani babban matsayi a cikin Roman Curia.

Ofishin yana da alhakin tantancewa da ba da shawarar 'yan takarar da suka cancanci zama bishop a duniya, inji rahoton NCR Online.

Wannan matsayin ya ƙara wa Prevost matsayi a idon duniya da kuma kara tasirinsa a cikin Cocin Katolika, wanda zai iya ɗaga martabarsa gabanin duk wani taron zaɓen Fafaroma.

Prevost ya zama Fafaroma na 267

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Robert Franis Prevost ya zama Ba'Amurke na farko da aka zaɓa a matsayin shugaban cocin Katolika na Duniya.

A rana ta biyu ta taron zaɓen Fafaroma, aka zabi Prevost matsayin sabon Fafaroma, matsayi mafi kololuwa a Kiristanci, kuma ya karɓi sunan Leo XIV.  

Bayan bayyanar farin hayaki daga dakin taro na St Peter, babban Kadinal, Dominique Mamberti ya sanar da zaben sabon Fafaroma ta hanyar furta kalmomin Latin: "Habemus Papam."

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »