Bincike: Abubuwa 2 da Suka Jawo Jirgi Ya Yi Hatsari Ɗauke da Shugaban Bankin Access

Bincike: Abubuwa 2 da Suka Jawo Jirgi Ya Yi Hatsari Ɗauke da Shugaban Bankin Access

  • Hukumar NTSB ta fitar da rahoto kan hatsarin jirgin Herbert Wigwe, wanda ya yi sanadin ajalinsa, matarsa, dansa da tsohon shugaban NGX
  • Rahoton ya ce matuƙin ya tashi jirgin duk da yanayi mara kyau, lamarin da ya jawo ya rasa gani da kuma kwacewar ikon jirgin daga hannunsa
  • NTSB ta kuma gano sakaci daga kamfanin jirgin, wanda ta ce ya gaza gyara wata na'ura tare kin cike bayanan da ke nuna halin da jirgin ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Hukumar kula da tsaro a bangaren sufurin Amurka (NTSB) ta fitar da rahotonta na ƙarshe kan hatsarin jirgi mai saukar angulu da ya yi sanadiyyar mutuwar Herbert Wigwe.

Herbert Wigwe shi ne, shugaban bankin Access, kuma hatsarin ya yi ajalin matarsa, Doreen; ɗansu na fari, Chizi; da Abimbola Ogunbanjo, tsohon shugaban kamfanin NGX.

Amurka ta fitar da rahoton abubuwan da suka jawo jirgin da ke dauke da shugaban bankin Access ya yi hatsari
Tsohon shugaban bankin Access, marigayi Herbert Wigwe | Jami'an NTSB suna duba jirgin Wige da ya yi hatsari. Hoto: @NTSB/X, Access Bank/Facebook
Asali: UGC

NTSB ta fitar da rahoto kan hatsarin jirgin Wigwe

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, hukumar NTSB ta alakanta hatsarin jirginda haɗuwar rashin iya aiki na matuƙi da kuma sakacin kamfanin jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Hatsarin, wanda ya faru a ranar 9 ga Fabrairu, 2024, kusa da iyakar Nevada a California, ya yi sanadiyyar mutuwar dukkanin fasinjoji shida da ke cikin jirgin mai lamba N130CZ.

Rahoton NTSB ya gano cewa babban dalilin hatsarin shi ne hukuncin matuƙin jirgin na tashi ƙarƙashin tsarin tashi VFR duk da fuskantar tangardar na'urar IMC.

An fahimci wannan ya sa matuƙin jirgin ya rasa sanin inda yake a sararin samaniya kuma daga ƙarshe ya rasa ikon sarrafa jirgin, wanda ya fado ƙasa.

Kuskuren matuki ya jawo rasa iko da jirgi

A cewar NTSB, mai yiwuwa matuƙin jirgin ya gamu da yanayi na rashin sanin matsaya, wanda ke faruwa lokacin da matuƙin jirgi ya kasa sanin alkiblar da yake tafiya a kai.

Rahoton ya ce a duk lokacin da matukin jirgi ya shiga cikin irin wannan yanayi na rashin tabbas, to galibi yana haifar da rasa ikon sarrafa jirgin.

Binciken ya jaddada cewa rashin iya sarrafa jirgin yadda ya kamata a cikin wannan yanayi shi ne babban dalili da ya jawo wannan mummunan hatsari, inji rahoton The Nation.

Baya ga matakin da matuƙin jirgin ya dauka na tashi, rahoton ya kuma nuna cewa akwai nakasu sosai a cikin tsarin tsaro da yanayin kulawar kamfanin jirgin.

Hukumar NTSB a Amurka ta yi bayani kan abin da ya jawo jirgin Habert Wigwe ya yi hatsari
Hon. Homendy, shugabar hukumar NTSB da ke Amurka. Hoto: @NTSB
Asali: Twitter

Sakacin kamfani wajen gyara na'urar jirgi

NTSB ta gano cewa kamfanin jirgin bai tabbatar da cewa matuƙan jirgin sun bi ƙa'idojin tsaro masu mahimmanci ba, ciki har da cike bayanai kan tashin jirgin da bayanin duk wata matsala da aka gani.

Ƙarin bayanai daga rahoton sun nuna cewa a lokacin tashi, matuƙin jirgin ya yi magana da daraktan kula da jirage (DOM) na kamfanin game da matsalar na'urar 'radar', wacce ta kasa aiki duk da ƙoƙarin gyara ta.

NTSB ta kuma bayyana cewa bayan isowa filin jirgi don ɗaukar fasinjoji, matuƙin jirgin da wani mai bin diddigin jiragen kamfanin sun yi waya amma sun kasa tattauna halin da na'urar 'radar' ke ciki.

Haka kuma ba su yi wata magana game da yanayin sararin samaniya a lokacin ba, wanda ake ganin wadannan dalilan biyu kan iya shafar ingancin aikin jirgin.

Dangote ya fashe da kuka a ta'aziyyar Wigwe

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Aliko Dangote, ya kasa ɓoye baƙin cikinsa na rasuwar Herbert Wigwe, tsohon shugaban bankin Access, aka ga yana kuka.

Bugu da ƙari, Dangote ya sanar da sauya sunan babbar hanyar da ta kai ga matatar man Dangote zuwa titin Herbert Wigwe, yana mai kiran Wigwe da "ginshiƙi" a rayuwarsa.

Herbert Wigwe ya rasu tare da matarsa da ɗansa, da kuma tsohon shugaban ƙungiyar canjin kuɗi ta Najeriya, a wani mummunan hatsarin jirgin sama a ƙasar Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »