Sabon Yaki Ya Barke a Tsakanin Kasashe 2, India Ta Fara Harba Makami Mai Linzami

Sabon Yaki Ya Barke a Tsakanin Kasashe 2, India Ta Fara Harba Makami Mai Linzami

  • Rahotanni sun bayyana cewa Indiya ta harba makamai masu linzami kan kasar Pakistan da Kashmir a ranar Laraba, 7 ga Mayu 2025
  • Indiya ta ce ta kai harin ne kan wurare tara na 'yan ta'adda a Pakistan, wadanda ta zarga da kai hari kan masu yawon bude ido a Kashmir
  • Sai dai Pakistan ta yi martani da cewa harin da Indiya ta kai ya yi ajalin fararen hula 26, yayin da iya kuma ta harbo jiragen yakin Indiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

India - A ranar Laraba, Indiya ta harba makamai masu linzami kan kasar Pakistan da kuma yankin Kashmir, inda Pakistan ke riƙe da shi.

Sai dai, kasar Pakistan ta ce ita ma ta harbo jiragen yaƙi biyar na Indiya a wannan faɗan mafi muni cikin shekaru 20 da suka gabata.

Indiya ta ce makamai masu linzami da ta harba kan Pakistan ya samu wuraren 'yan ta'adda
Sojojin Pakistan suna duba barnar da harin Indiya ya haifar. Hoto: AFP
Asali: AFP

India ta kai sabon hari kan kasar Pakistan

Hare-haren da Indiya ta kai a lardin Punjab, mafi yawan jama'a a Pakistan shi ne na farko tun bayan yaƙinsu na fiye da rabin karni da ya gabata, inji rahoton Al-Jazeera.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Wannan harin na ranar Laraba, ya haifar da fargaba mai tsanani a tsakanin mazauna kasashen biyu, inda ake tsoron komawa gidan jiya.

Indiya ta ce ta kai hari kan wurare tara na "ƙungiyoyin ta'addanci" a Pakistan, inda ake zargin wasu daga cikinsu na da alaƙa da harin da aka kai wa 'yan yawon buɗe ido na Hindu.

An ce harin da 'yan ta'addan suka kai ya yi ajalin masu yawon bude ido 26 a Kashmir ta Indiya a watan da ya gabata.

Tun da farko Indiya ta ce biyu daga cikin mutane uku da ake zargi da hannu a harin 'yan Pakistan ne amma ba ta bayyana wata shaida ba, zargin da Pakistan ta karyata.

Harin India ya yi ajalin fararen hula 26 a Pakistan

Sai dai kuma, Islamabad ta ce harin da Indiya ta kai ya shafi wurare shida na Pakistan, kuma babu daya daga cikinsu da ya kasance sansanin 'yan ta'adda.

Kakakin sojin Pakistan ya ce aƙalla fararen hula 26 ne suka mutu kuma 46 suka ji rauni a harin makamai masu linzami da Indiya ta kai masu.

Amma wasu masu magana da yawun sojin Indiya biyu sun dage kan cewa sojojin Indiya sun kai hari kan wuraren da ke da alaƙa da ƙungiyoyin 'yan ta'addar Islama Jaish-e-Mohammed da Lashkar-e-Taiba ne.

A zantawa da manema labarai a New Delhi, sojojin sun ce an kai hare-haren ne kan "sansanonin 'yan ta'adda" waɗanda suka zama cibiyoyin daukar sababbin mayaka, kai hare-harei, da adana makamai.

"Pakistan na shirin kai wa India hari" - Misri

Sun ce sojojin Indiya sun yi amfani da makamai masu fasaha don guje wa ɓarnar da za ta iya shafar fararen hula da ababen more rayuwa na farar hula, amma ba su yi bayani dalla-dalla kan takamaiman hanyoyin da aka yi amfani da su a hare-haren ba.

Sakataren harkokin wajen Indiya, Vikram Misri, ya ce:

"Bayanan sirri kan ƙungiyoyin ta'addanci da ke Pakistan sun nuna cewa ana shirin kai wasu hare-hare kan Indiya, don haka ya zama dole a ɗauki matakan kariya cikin gaggawa."

A taron manema labarai na haɗin gwiwa da sojojin Indiya da ma'aikatar harkokin waje suka shirya, an lissafa hare-haren da 'yan ta'addar Pakistan suka kai Indiya.

Misri ya ce Pakistan ba ta yi komai ba game da "ƙungiyoyin ta'addancin" bayan harin da aka kai wa 'yan yawon buɗe ido na Kashmir.

Pakistan ta ce ta harbo jiragen yakin India guda 5
Sojojin Pakistan suna duba barnar da harin Indiya ya haifar. Hoto: AFP
Asali: AFP

Pakistan ta harbo jiragen yakin Indiya 5

Pakistan ta ce makamai masu linzami da Indiya ta harbo masu sun afka kan wurare uku kuma kakakin soji ya shaida wa kafar Reuters cewa an harbo jiragen Indiya biyar.

Sai dai kuma, majiyoyin gwamnatin yankin guda huɗu a Kashmir ta Indiya sun shaida wa kafar labaran cewa jiragen yaƙi uku sun yi karo a yankuna daban-daban na yankin Himalayan.

Majiyoyin sun ƙara da cewa an kwantar da dukkanin matuƙan jirgin uku a asibiti, lamarin da jami'an ma'aikatar tsaron Indiya ba su iya tabbatar da rahoton ba.

Indiya da Pakistan ba sa ga maciji

Tun da fari, mun ruwaito cewa, ana fargabar sabon faɗa zai barke tsakanin Indiya da Pakistan, waɗanda ake ganin kamar 'yan uwa ne amma masu bakar gaba da juna.

An ce wannan rigimar tasu ta samo asali tun bayan da Musulmi suka musuluntar da yammacin kasar, suka hana bautar gumaka.

Turawa sun raba ƙasar, Musulmi suka samu rabi, Hindu ma suka samu rabi, amma Indiya ta riƙe wasu wurare masu arziƙi da Pakistan ke neman iko a kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »