Bayan Sa'oi 30, an Gaza Kawo Karshen Gobarar da Ta Tashi a Isra'ila

Bayan Sa'oi 30, an Gaza Kawo Karshen Gobarar da Ta Tashi a Isra'ila

  • Gobarar da ta tashi a dajin kusa da birnin Jerusalem a Isra’ila ta yi barna mai yawa, yayin da ake kokarin shawo kanta
  • An tura jiragen kashe gobara daga kasashen Turai yayin da Netanyahu ya bayyana lamarin a matsayin abu mai hadari
  • Gwamnatin kasar Isara'ila ta tabbatar da cewa ta kama akalla mutum 18 bisa zargin su da kunna wutar da gangan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Israel - Hukumar kashe gobara ta Isra’ila ta ce ana kokarin shawo kan wutar da ta tashi a dazukan kusa da Jerusalem, wadda ta dauki tsawon sa'o'i 30 ana kokarin dakile ta.

Wutar ta kone sama da hekta 5,000 ciki har da hekta 3,000 na daji tun daga ranar Laraba da yamma, lamarin da ya jefa dubban mutane cikin firgici da barin muhallansu.

Israila
Ana kokarin kashe gobarar Isra'ila. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Rahoton Independent ya nuna cewa Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu ya bayyana gobarar a matsayin matsalar gaggawa ta kasa, inda ya nemi taimako daga kasashen duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Kasashen Turai sun aike da taimako Isra'ila

A kokarin dakile yaduwar wutar, jiragen kashe gobara daga kasashen Girka, Cyprus, Croatia da Italiya sun isa Isra’ila domin bayar da agajin gaggawa.

Rahotanni sun ce kasashen Ukraine, Spain da Faransa su ma sun yi alkawarin turo da taimako cikin gaggawa.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da musabbabin tashin wutar ba. Amma Firaminista Netanyahu ya ce an kama mutane 18 da ake zargi da kunna wutar da gangan.

Netanyahu
An kama wasu mutane bisa zargin kunna wuta a Isra'ila. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Yadda aka fara gobarar daji a kasar Isra'ila

Jami’an ‘yan sanda sun ce gobarar ta fara ne a kusa da babban titin da ya hada biranen Jerusalem da Tel Aviv.

Rahoton Al-Jazeera ya bayyana cewa saboda haka ne aka rufe hanyar tare da kwashe dubban mutane daga yankunan.

Amma bayan aikin dare da rana daga jami’an kashe gobara sama da 150 da kuma jiragen sama 12, an an fara dakile yaduwar wutar a wasu yankuna.

A sanarwar da ‘yan sanda suka fitar, sun bayyana cewa an bude dukkan hanyoyin da aka rufe domin bai wa jama’a damar dawowa gidajensu.

Mutane da dama sun jikkata a gobarar Isra'ila

Akalla mutane 12 ne aka kwantar da su a asibiti saboda gobarar, yayin da wasu 10 aka yi musu jinya a wurin da abin ya faru.

Babban kwamandan hukumar kashe gobara na yankin Jerusalem, Shmulik Friedman, ya ce:

“Wannan na iya zama gobara mafi girma da aka taba fuskanta a tarihin kasar.”

Kazalika, kamfanin watsa labarai na kasar Isra’ila ya tabbatar da cewa ma’aikatan kashe gobara 17 sun samu raunuka yayin aikin ceto.

An soki Filato kan alaka da Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan Najeriya, Femi Fani Kayode ya caccaki gwamnatin Filato kan kulla alaka da Isra'ila.

Femi Fani Kayode ya ce bai kamata gwamnatin jihar Filato ta kulla alaka da kasar da ta shahara da zalunci ba.

Tsohon ministan ya yi magana ne yayin da 'yan bindiga suka yawaita kai hare hare a wasu kananan hukumomin jihar Filato.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »